Jaridar tattalin arziki ta duniya ta yi hasashen faduwar Buhari a zaben 2019
Sashen tattara bayanan sirri na jaridar tattalin arziki na Duniya,The Economist ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ne zai iya kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Hasashen ya bayyana ne sa’o’i 24 bayan gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi gargadin cewa kada su sakankance da cewar za su iya kayar da PDP cikin sauki.
Haka kuma ya na zuwa ne watanni biyu bayan da jaridar ta yi hasashen faduwar shugaban kasar a zaben mai zuwa.

Asali: Facebook
Hasashen ya fito ne a wani rahota da jaridar ta fitar game da Najeriya mai dauke da kwanan wata 17 ga watan Oktoba.
Wasu daga cikin dalilan da jaridar ta bayyana na faruwar hakan sun hada da alkawuran da Atiku ya yi na samar da ayyukan yi da rage talauci, wadanda sune manyan matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a karkashin gwamnatin Buhari.
KU KARANTA KUMA: Yan Nigeria sun maidawa Buhari martani kan gazawarsa na gabatarwa INEC takardunsa
Jaridar ta ce Buhari da Atiku za su raba kuri’un Arewa inda mafi yawan magoya bayan Buhari su ke da zama, sannan kuma cewa Atiku zai lashe kuri’un kudancin kasar nan inda dama PDP ta fi karfi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng