NDLEA: Kafin haramta 'Codeine', Kano, Jigawa sun sha kwalba Miliyan 3

NDLEA: Kafin haramta 'Codeine', Kano, Jigawa sun sha kwalba Miliyan 3

- Hukumar NDLEA ta ce akalla kwalaben maganin tari mai dauke da sinadarin codeine miliyan 3 ne aka kwankwade a jihohin Kano da Jigawa, kafin daga bisani aka haramta sayar da shi

- Da ya ke jawabi a wani bukin lalata tan 6.21 na muggan miyagun kwayoyi a garin Dutse, Kanal Mustapha ya ce sama da kilogram 253 na kwayar tramol ne hukumar ta cafke a iyakar Maigatari

- Itama da take jawabi, shugabar hukumar NDLEA a jihar Jigawa, Josephine Ruth, ta bayyana cewa hukumar ta cafke mutane 3,608 da ake zargi tare da kwace tan 8.26 na muggan kwayoyi

Babban shugaba kuma babban jami'in hukumar da ke yaki da tu'ammali da muggan miyagun kwayoyi da kayan maye, NDLEA, Kanal Muhammad Mustapha, (mai ritaya) ya bayyana cewa akalla kwalaben maganin tari mai dauke da sinadarin codeine miliyan 3 ne aka kwankwade a jihohin Kano da Jigawa, kafin daga bisani aka haramta sayar da shi.

Da ya ke jawabi a wani bukin lalata tan 6.21 na muggan miyagun kwayoyi a garin Dutse, Kanal Mustapha ya ce sama da kilogram 253 na kwayar tramol ne hukumar ta samu nasarar cafkewa a iyakar garin Maigatari.

"Babban makasudin wannan buki shine tabbatar da cewa duk wasu muggan kwayoyi da hukumar ta kwace an lalata su don gujewa sake fadawa cikin jama'a, da kuma kiyaye al'umma daga sharrin kwayoyin.

KARANTA WANNAN: Rundunar sojin Nigeria da ta kasar Kamaru sun kulla wata yarjejeniya

NDLEA: Kafin haramta 'Codeine', Kano, Jigawa sun sha kwalba Miliyan 3
NDLEA: Kafin haramta 'Codeine', Kano, Jigawa sun sha kwalba Miliyan 3
Asali: Twitter

"Haka zalika, zai taimaka wajen wayarwa masu ruwa da tsaki kai, kasancewar a gabansu ne za a lalata kwayoyin, wanda kuma zai aika babban sakon gargadi ga duk masu safarar kwayoyin na cewar hukumar NDLEA zata ci gaba da lalata wannan mummunan kasuwancin nasu," a cewar shugaban hukumar.

Itama da take jawabi, shugabar hukumar NDLEA a jihar Jigawa, Josephine Ruth, ta sha alwashin dakile safarar mugan kwayoyi da kuma rage yawan bukatar kwayoyin da tallafin gwamnatin jihar Jigawa da kuma sauran hukumomi na jihar.

NDLEA: Kafin haramta 'Codeine', Kano, Jigawa sun sha kwalba Miliyan 3
NDLEA: Kafin haramta 'Codeine', Kano, Jigawa sun sha kwalba Miliyan 3
Asali: Facebook

Ta bayyana cewa hukumar ta cafke mutane 3,608 da ake zargi tare da kwace tan 8.26 na muggan kwayoyi a nau'i'i daban daban.

A cewarta, "Wannan taro da muke gudanarwa a yau, ya jaddada irin kokarinmu na bin umurnin da babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Dutse, na lalata kwayoyin da hukumar ta kwace ta hanyar kona su gaba daya."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng