Tozarci ne karara kalaman Buhari na 'Yan Nigeria masu wata to su koma can' - PDP
- Jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya ce duk 'yan Nigeria da suka ga suna da wata kasa, to su tattara su koma can
- Ta kuma ce, "hakan ya nuna cewa ba zai iya shugabantar jama'a ba, kuma ba shi da waraka ga matsalolin da kasar ke fuskanta"
- PDP ta ce kowa na kokarin jure wahalar rayuwar da ake ciiki, tsananin yunwar da ke sa har mutane suna mutuwa wanda a cewarsa gwamnatin Buhari ce ta ja hakan
Jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya ce duk 'yan Nigeria da suka ga suna da wata kasa, to su tattara su koma can. PDP ta bayyana wannan kalami a matsayin cin fuska ga kujerar shugaban kasa, da kuma tsantsar nuna rashin iya mulki.
Da wannan kalamin, jam'iyyar ta ce shugaban kasar ya yi magana kamar wani wanda baida sauran katabus ga al'ummar da ya ke shugabanta.
KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Sahle-Work Zewde ta zama shugabar kasa mace ta farko a kasar Ethiopia
Sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa, Mr Kola Ologbondiyan, a cikin wata sanarwa da ya bayar a Abuja a ranar Laraba, ya ce shugaban kasa Buhari, a kalaman da ya yi na cewar, "Wadanda duk suke ganin suna da Wata kasar, to su tattara su koma can", ta kuma ce, "hakan ya nuna cewa ba zai iya shugabantar jama'a ba, kuma ba shi da waraka ga matsalolin da kasar ke fuskanta."

Asali: Twitter
Mr. Ologbondiyan ya bayyana kalamin shugaban kasar a matsayin "Rashin nuna dattako" da kuma cin fuska ga Miliyoyin yan Nigeria, wanda ya ce, kowa na kokarin jure wahalar rayuwar da ake ciiki, tsananin yunwar da ke sa har mutane suna mutuwa wanda a cewarsa gwamnatin Buhari ce ta ja hakan."
Ologbondiyan ya ce wadannan manyan matsalolin da ke fuskantar yan Nigeria su ne suka tilasta mutane gudanar da ayyukan kunar bakin wake don ganin sun samawa kansu da iyalansu abubuwan da zasu yi amfani da su don rayuwar yau da kullum.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng