EFCC ta bayyana matsayin ta akan binciken Oshiomhole

EFCC ta bayyana matsayin ta akan binciken Oshiomhole

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta mayar da raddi game da karar da wani dan asalin jihar Edo ya shigar kotu, ya na kalubalantar hukumar saboda ya nemi ta binciki tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole, amma hukumar ta kau da kai a kan sa.

A korafin da ya shigar, Mista Ochie ya nemi kotu ta tilasta wa hukumar bincikar Oshimhole akan zargin sad a harkalla da wawurar makudan kudade da ya yi masa, kuma ya gabatar da takardun shaidar cin kudaden a gaban EFCC, amma hukumar ta kau da kan ta.

Wannan rokon da ya yi wa kotun ne ya sa ita Babbar Kotun Tarayya ta Abuja din ta aza ranar Talatar da ta wuce a matsayin ranar da za a fara sauraren kara, kuma aka ce an aika wa kowace bangare sammacin sanarwa.

Yayin da lauyan Oshimhole ya bayyana a kotu a ranar Talatar da ta gabata, babu wani lauya daga bangaren EFCC da ya je kotun.

EFCC ta bayyana matsayin ta akan binciken Osinbajo
EFCC ta bayyana matsayin ta akan binciken Osinbajo
Asali: Depositphotos

A kokarin kare Oshiomhole da lauya ya yi tun da fari, ya yi kokarin hana a binciki shi shugaban APC din na kasa baki daya, a bisa dalilin cewa wa’adin caje-cajen da ake yi wa wanda ya ke karewa din ya wuce.

Sai dai kuma a na ta bangaren, EFCC ta ce ta ki zuwa kotun ne saboda wanda ya shigar da karar bai aika mata bayanan abin da kotun ta zartas ba.

KU KARANTA KUMA: INEC za ta sanar da yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki a yau

A baya kotu ta tilasta wa EFCC cewa tilas ta karbi takardun korafin da aka kai mata kan zargin wawurar kudaden da ake yi wa Oshimhole ta bincike shi kuma ta gurfanar da shi.

Amma sai Oshimhole ya kai kara wata kotun inda ya nemi a hana EFCC bincikar sa din da waccan kotun ta ce sai an yi.

Kakakin EFCC Wilson Uwejaren ya nuna damuwar sa kan yadda lauyan mai shigar da kara, West Idahosa ya yi wa kotu ikirarin cewa ya aika wa EFCC bayanan da ya kamata ya aika mata.

Ya ce da an aika wa EFCC da kwafen bayanan, da wakilin ta ya bayyana a kotun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng