Babu karya a cikin bidiyon Ganduje yana karbar cin hancin $5m - Amsar Jaafar ga majalisar Kano

Babu karya a cikin bidiyon Ganduje yana karbar cin hancin $5m - Amsar Jaafar ga majalisar Kano

- Mawallafin jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya bayyana gaban majalisar dokoki ta jihar Kano, da ke bincike kan zargin da ake yiwa gwannan jihar Kano

- A hannu daya kuwa, gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewar bidiyon ba na gaskiya bane, an yi amfani da kwamfuta wajen hada shi

- A ranar Alhamis dinnan ne, Mr Jaafar ya tsaya gaban majalisar, tare da yin rantsuwa akan cewa bidiyon na gaskiya ne ba hada shi akayi ba

Mawallafin jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya bayyana gaban majalisar dokoki ta jihar Kano, da ke bincike kan zargin da ake yiwa gwannan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na karbar cin hancin $5m daga hannun 'yan kwangila.

Jaridar Premimum Times ta wallafa labarai daga bidiyon, wanda ta same shi daga Daily Nigerian, da ke nuna lokaci, waje da kuma yadda gwamnan jihar Kanon ke karbar daloli a matsayin cin hanci a wurare daban daban. Kudaden da Ganduje ya karba dai sun kai dalar Amurka miliyan biyar, daga hannun 'yan kwangilar jihar.

KARANTA WANNAN: Ya zama wajibi ka kori babban sakataren NHIS - Kungiyar kwadago ta farwa Buhari

Haka zalika gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewar bidiyon ba na gaskiya bane, an yi amfani da kwamfuta wajen hada shi, sai dai wani kwararre ya tabbatar da sahihancin bidiyon.

Babu karya a cikin bidiyon Ganduje yana karbar cin hancin $5m - Amsar Jaafar ga majalisar Kano
Babu karya a cikin bidiyon Ganduje yana karbar cin hancin $5m - Amsar Jaafar ga majalisar Kano
Asali: Depositphotos

A ranar Alhamis dinnan ne, Mr Jaafar ya tsaya gaban majalisar, tare da yin rantsuwa akan cewa bidiyon na gaskiya ne ba hada shi akayi ba.

A yayin da ake jefa masa tambayoyi, Jaafar yaki bayyana wanda ya samar masa da bidiyon, wanda ke nuna Ganduje a lokacin da yake karbar cin hanci daga 'yan kwangilar jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng