Rikicin Kaduna: El-Rufai ya yi barazanar daukar mataki a kan sarakunan gargajiya
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da sarakunan gargajiya sun gana a ranar Talata, 23 ga watan Oktoba kan rikicin da ya afku a ranar Lahadin da ya gabata.
El-Rufai ya sha alwashin yin amfani da dokokoki daban-daban da suka sanya kudi kan garuruwan da suka bayar da damar wanzar da rikici domin habbaka rikice-rikicen jihar Kaduna.
Gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta samar da cikakken bayanan dokokin.

Source: UGC
El-Rufai ya gargadi sarakunan na gargajiya cewa gwamnati ba za ta amince da wani uziri daga gare su ba lokacin da rikici ya barke a garuruwan su.
KU KARANTA KUMA: Keyamo ya ce lallai Atiku mutun ne mai rashawa a gaban kwamitin majalisar dattawa
El-Rufai ya bayyana cewa gwamnati na aiki tare da rundunar yan sandan jihar Kaduna domin samar da sashin yan sanda a Narayi da Sabon Tasha.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng