Hadimin wani gwamnan PDP ya yi murabus ya kuma fice daga jam’iyyar

Hadimin wani gwamnan PDP ya yi murabus ya kuma fice daga jam’iyyar

Idorenyin Esikot, hadimin Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom ya yi murabus daga matsayinsa.

Mista Esikot ya fada ma majiyarmu ta Premium Times a ranar Talata, 23 ga watan Oktoba cewa tun a watan Satumba yayi murabus.

Yana daya daga cikin hadimai shida da suka yi murabus a gwamnatin zuwa yanzu a daidai lokacin da guguwar zaben 2019 ke sake gabatowa.

Ana sanya ran hakan zai sa zaben jihar ya zafafa a tsakanin jam’iyya mai mulki a jihar wato Peoples Democratic Party (PDP) da kuma All Progressives Congress (APC) mai adawa a jihar.

Hadimin wani gwamnan PDP ya yi murabus ya kuma fice daga jam’iyyar
Hadimin wani gwamnan PDP ya yi murabus ya kuma fice daga jam’iyyar
Asali: Twitter

Daya daga cikin hadimanan gwamnan da suka yi murabus a watan Satumba, Anietie Ebe ta fada ma majiyar tamu cewa hadiman gwamnan da dama za su bar gwamnatin kafin zaben 2019.

A cewar Esikot ya ce ya yi murabus ne saboda abu tallafi ta ko ina.

Ya ce wasu lokutan da kudinsa yake siyawa yan kasuwa abun motsa baki yayinda za su yi ganawar gwamnati. Kuma cewa gwamnatin ba ta taba sauraren koke-kokensa ba.

KU KARANTA KUMA: Makokin 40: 'Yan shia zasu fara machi zuwa zaria daga birane a qafa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta jaddada cewa ta aika da sunayen 'yan takararta ga hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.

A cikin wata sanarwa da ta fitar da ke bayani kan kalubalen da ta fuskanta a wasu jihohi, Jam'iyyar ta ce tana da 'yancin mika sunayen 'yan takararta na Zamfara kuma hakkin hukumar zabe ne ta amsa.

Ta ce hukumar zabe ba za ta iya hana wa 'yan takararta shiga zabe ba a Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng