Da dumin sa: 'Yan sanda sun cafke mutumin da ya hau dogon karfe saboda tsanar mulkin Buhari

Da dumin sa: 'Yan sanda sun cafke mutumin da ya hau dogon karfe saboda tsanar mulkin Buhari

- 'Yan sanda sun cafke mutumin da ya hau dogon karfe saboda tsanar mulkin Buhari

- Shi kuma yace yaudarar sa sukayi ya sauko

- Yace da sun sake shi zai koma

Labarin da muke samu na nuni ne da cewa wannan mutumin mai suna Lawal Faro da aka kiyasta shekarun sa da kusan 40 da kuma akace ya haye dogon karfe har sai Shugaba Buhari ya dawo yanzu haka yana hannun 'yan sanda.

Da dumin sa: 'Yan sanda sun cafke mutumin da ya hau dogon karfe saboda tsanar mulkin Buhari
Da dumin sa: 'Yan sanda sun cafke mutumin da ya hau dogon karfe saboda tsanar mulkin Buhari
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An zargi gwamnonin APC 4 da cin dunduniyar Buhari

Kamar dai yadda muka samu, Lawal Faro yanzu haka yana a ofishin 'yan sanda na garin Jimetan Yola inda yake ansa tambayoyi game da abun da yayi.

Legit.ng Hausa ta samu cewa da yake karin haske game da yadda lamarin ya auku, Lawal Faro ya ce wasu 'yan sanda suka yaudare shi suka ce ya sauko za su kai shi wajen Atiku amma yana saukowa sai kawai suka kama shi.

Ya kara da cewa shi har yanzu bai daddara ba, da zarar sun sake shi zai koma saman karfen kuma kamar yadda yayi alkawari, sai dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya tabbatar masa da cewa zai hambarar da gwamnatin Buhari sannan zai sauko.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng