Daga karshe: Shugaban kasar Ethiopia, Mulatu ya yi murabus

Daga karshe: Shugaban kasar Ethiopia, Mulatu ya yi murabus

- Shugaban kasar Ethiopia, Mulatu Teshome ya rubuta takardar murabus dinsa, inda ya aikawa hadakar majalisun dokokin kasar bukatar ajiye mulkin nasa

- Hadakar majalisun dokoki na kasar, za su duba wanda ya cancanci ya gaji kujerar tashi, a wani zama da suka shirya gudanarwa a yau Alhamis

- Murabus din Teshome, ya zo jim kadan bayan da aka samun sauyi a jami'an gwamnatin kasar Ethiopia

Rahotannin da Legit.ng ta samu daga kamfanin dillancin labarai na kasar Ethiopia, ENA, na nuni da cewa a ranar Laraba, shugaban kasar Ethiopia, Mulatu Teshome ya rubuta takardar murabus dinsa, inda ya aikawa hadakar majalisun dokokin kasar bukatar ajiye mulkin nasa.

Teshome, wanda ya kasance a shugabancin kasar tun a watan Oktoba, 2013, ya aikewa hadakar majalisun dokokin kasar takardar murabus dinsa, wadanda ake sa ran zasu yi zama na musamman don duba takaradar tare da tunanin gudanar da zaben sabon shugaban kasa.

Hadakar majalisun dokoki na kasar, za su kuma duba wanda ya cancanci ya gaji kujerar tashi, a wani zama da suka shirya gudanarwa a yau Alhamis, kamar yadda rahoton ya bayyana.

KARANTA WANNAN: Fayemi ya amince da sakin N200m don sayawa malaman jihar Ekiti motoci da gidaje

Daga karshe: Shugaban kasar Ethiopia, Malatu ya yi murabus
Daga karshe: Shugaban kasar Ethiopia, Malatu ya yi murabus
Asali: Depositphotos

Zaman da hadakar majalisun dokokin kasar zasu gudanar a ranar Alhamis, "zai baiwa majalisun damar dubin tsanaki kan wannan takardar murabus da kuma batu kan sake zabar sabon shugaban kasa," a cewar rahoton ENA.

Shugaban kasar mai barin gado, wanda ya yi karatun daftari a harkokin sanin dokokin kasashe a jami'ar Peking ta ke birnin Sin, an nada shi shugaban kasar Ethiopia a ranar 7 ga watan Oktoba, 2013 yayin da ya ke aiki a matsayin jakadan kasar Ethiopia a kasar Turkiya.

Teshome ya kasance mamba a jam'iyyar Oromo Democratic Party (ODP), kuma daya daga cikin shuwagabanni 4 na jam'iyya mai mulki ta People’s Revolutionary Democratic Front (EPRDF).

Murabus din Teshome, ya zo jim kadan bayan da aka samun sauyi a jami'an gwamnatin kasar Ethiopia.

Teshome, mai shekaru 63, ya yi aiki a matakan gwamnati da dama a kasar Ethiopia, a ofisoshi da ma'aikatu musamman mukamin da ya rike na mataimakin ministan ma'aikatar bunkasa tattalin arzikin kasar, ministan noma da kuma mai magana da yawun fadar shugaban kasar.

Ya kuma taba yin aiki a matsayin wakilin Afrika ta Gabas a kasar Sin, Turkiya, Japan, Thailand da kuma Azerbaijan a bangaren jakadan diflomasiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng