'Yan sandan Najeriya sun soma binciken kisan manyan malaman addini a Najeriya

'Yan sandan Najeriya sun soma binciken kisan manyan malaman addini a Najeriya

Jami'an 'yan sandan Najeriya, shiyyar jihar Abia dake a yankin kudu maso gabashin Najeriya a ranar litinin din da ta bata ta sanar da soma wani kwakkwaran bincike akan kisan gillar da aka yi wa wasu manyan malaman addinin kirista a garin Umuobia a watannin baya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar a jihar, SP Geoffrey Ogbonna shine ya sanar wa da majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai hakan a garin Umuahia, babban birnin jihar ta Abia.

'Yan sandan Najeriya sun soma binciken kisan manyan malaman addini a Najeriya
'Yan sandan Najeriya sun soma binciken kisan manyan malaman addini a Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Kotu ta yanke hukunci game da batun kamo shugaban hukumar INEC

Legit.ng Hausa ta samu cewa manyan malaman da aka kashe sun hada da Fasto Kelechi Iwuanyanwu da ke shugabantar majami'ar Winds of Glory, da kuma Fasto Ogbonna.

A wani labarin kuma, Wani rahoto da muka samu daga majiyar mu ta ThisDay yana nuni ne da cewa masu fada aji na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Legas sun dage kan lallai lallai sai an tsige gwamnan jihar Akinwunmi Ambode kafin zaben 2019.

Haka ma dai rahoton ya bankado cewa tuni ma har shire-shire sun kammala na tabbatar da tsige gwamnan da zarar kurar zabukan fitar da gwanin nan ta dan lafa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng