Makiyin ka na gindin ka: An zargi wasu gwamnonin APC 4 da shirya wa Buhari gadar zare
Shugaban wata kungiya dake rajin kare muradun gwamnatin shugaba Buhari da kuma fafutukar ganin ya lashe zaben shekarar 2019 watau Federation of Buhari Support Group, mai suna Ibrahim Sikiru yace sun gano wasu gwamnonin APC 4 da ba su son Buhari.
Ibrahim Sikiru, wanda ya ce gwamnonin da ke yi wa kan su lakani da masu ra'ayin 'yan mazan jiya, gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ne ke jagorantar makarkashiyar cin dunduniyar shugaba Buhari din.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kashe wani basarake a Arewa
Legit.ng Hausa ta samu cewa sauran gwamnonin da kungiyar ta zarga da yi wa shugaban kasar zagon kasa sun hada da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun, Gwamna Ahmad Nasir el-Rufai na jihar Kaduna, da kuma Gwamna Jubrilla Bindow na jihar Adamawa.
Daga nan ne kuma sai shi shugaban kungiyar ya sake tabbatar wa da shugaban kasar aniyar sa da mambobin kungiyar su na yin aiki tukuru domin samun nasara a zaben 2019.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng