APC ta kori tsohon Sakataren gwamnatin daga cikin ta

APC ta kori tsohon Sakataren gwamnatin daga cikin ta

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Enugu dake a Kudu maso gabashin Najeriya ta fitar da sanarwar korar daya daga cikin jiga-jigan ta kuma tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Cif Onyemauche Nnamani bisa laifukan rashin da'a.

Wannan matakin dai na jam'iyyar ya biyo bayan wata sanarwa da shugaban jam'iyyar ta APC na jihar ta Enugu, Dakta Ben Nwoye.

APC ta kori tsohon Sakataren gwamnatin daga cikin ta
APC ta kori tsohon Sakataren gwamnatin daga cikin ta
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Dalilin da yasa bamu kaunar Buhari - Gwamnan Benue

Legit.ng Hausa ta samu cewa shi dai Dakta Ben, ya ce a matsayin su na shugabannin jam'iyyar a matakin jiha sun yanke shawarar korar ta sa ne biyo bayan kai jam'iyyar da yayi kotu ba tare da ya tuntube su ba ko kuma jin ba'asi.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya, shiyyar jihar Abia dake a yankin kudu maso gabashin Najeriya a ranar litinin din da ta bata ta sanar da soma wani kwakkwaran bincike akan kisan gillar da aka yi wa wasu manyan malaman addinin kirista a garin Umuobia a watannin baya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar a jihar, SP Geoffrey Ogbonna shine ya sanar wa da majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai hakan a garin Umuahia, babban birnin jihar ta Abia.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng