Wanda ya haye kan dogon karfe ya yi barazanar dirowa kasa muddin Buhari bai yi murabus ba

Wanda ya haye kan dogon karfe ya yi barazanar dirowa kasa muddin Buhari bai yi murabus ba

- Lawan Faro, ya hau saman karfen allon sanarwa mai tsayin mita 40, inda kuma ya yi barazanar dirowa kasa muddin Buhari bai yi murabus ba

- Faro ya ce ya yanke wannan hukunci na hawa kololuwar karfen allon sanarwar ne duba da irin matsanancin talauci da ya addabi kasar

- Ya ce lokaci ya yi da shugaban kasa Buhari zai baiwa mutane irinsu Atiku Abubakar wuri don su jagoranci Nigeria

Lawan Faro, wani matashi a Yola, babban birnin jihar Adamawa, ya hau saman karfen allon sanarwa mai tsayin mita 40, inda kuma ya sha alwashin durowa don kashe kansa, ma madamar shugaban kasa Muhammadu Buhari bai yi murabus a cikin awanni 12.

Da yake zantawa da jaridar SaharaReporters, Faro ya ce ya yanke wannan hukunci na hawa kololuwar karfen allon sanarwar ne duba da irin matsanancin talauci da ya addabi kasar ta Nigeria, karkashin gwamnatin Buhari.

"Ina ga lokaci ya yi da shugaban kasa Buhari zai baiwa mutane irinsu Atiku Abubakar wuri don su jagorancemu, duba da irin tsananin rayuwa da jama'a ke fuskanta a gwamnatinsa," a cewarsa.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Buhari za ta kayyade adadin 'yayan da kowacce uwa zata haifa

Wanda ya haye kan wani dogon karfe ya yi barzanar dirowa kasa muddin Buhari bai yi murabus ba
Wanda ya haye kan wani dogon karfe ya yi barzanar dirowa kasa muddin Buhari bai yi murabus ba
Asali: Twitter

Ya yi barazanar cewa zai duro daga saman karfe nan da awanni 12 ma damar Atiku bai bayyana a gabansa ya bashi tabbacin zai doke Buhari a babban zabe na 2019 ba.

"Zan ci gaba da zama a saman karfen nan har nan da awanni 12 don nuna bakin cikina akan mulkin Buhari, ma damar Atiku bai bayyana a gabana ya bani tabbacin cewa zai tunbuke Buhari a zabe mai zuwa ba to kuwa zan duro in kashe kaina."

A bangare daya kuwa, dandazon jama'a sun taru a karkashin allon tallace tallacen suna ihun "Sai Baba Buhari!"

Wannan mataki da Faro ya dauka ya yi kama da na Nura Ilyasu, mutumin da ya dare saman karfen Mass a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a watan da ya gabata, inda ya ke barazanar durowa ma damar Buhari ya dage sai ya sake tsayawa takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng