Yanzu Yanzu: An kashe mutane 12 a Adamawa bayan kisan yan banga 3

Yanzu Yanzu: An kashe mutane 12 a Adamawa bayan kisan yan banga 3

Mumunan rikici a Lafiya karamar hukumar Lamurde da ke jihar Adamawa a ranar Talata, 23 ga watan Oktoba yayi sanadiyar mutuwar mutane goma sha biyu ciki harda ‘yan banga uku.

Anyi zargin cewa tarin mutane da yawa sun mutu sakamakon wani rikici da ya barke a ranar Talata, 23 ga watan Oktoba a Lafiya karamar hukumar Lamurde dake jihar Adamawa.

Majiya daga mazauna yankin sun fada ma Sahara Reporters cewa rikicin ya fara ne bayan an kashe wasu yan banga uku da suka yi kokarin kawo karshe rikicin manoma a cikin daji.

Yanzu Yanzu: An kashe mutane 12 a Adamawa bayan kisan yan banga 3
Yanzu Yanzu: An kashe mutane 12 a Adamawa bayan kisan yan banga 3
Asali: Depositphotos

Wani idon shaida wanda ya bayyana sunansa a matsayin Mohammed Sani wanda ya shad a kyar ya sanar da manema labarai cewa rikicin ya barke ne a yammacin ranar Talata a Lafiya bayan an tsinci gawar wani mazaunin garin a gonarsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: APC da PDP sun sake asarar wasu mambobinsu na majalisar wakilai

Othman Abubakar, kakakin yan sandan jihar ya tabbatar da lamarin ga manema labarai amma ya ki bayar da wani cikakken bayani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng