Yanzu Yanzu: Sanata Shehu Sani ya koma jam’iyyar PRP
Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a ranar Talata, 23 ga watan Oktoba ya koma jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP), kwanaki uku bayan ya bar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Sani ya bayyana hakan a wata sanarwa daga mai bashi awara a harkokin siyasa, Mista Suleiman Ahmed a Abuja.
Ya bayyana cewa ba zai taba yiwuwa ba sanatan ya ci gaba da tafiya da tsarin siyasar APC mara alkila ba.

Asali: Twitter
Da yake tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a wani hira shugaban jam’iyyar na jihar Kaduna, Dr Tom Maiyashi yace a yanzu dan majalisar ya zama mamban jam’iyyarsu.
KU KARANTA KUMA: Har yanzu cin hanci da rashawa ne babban matsalarmu - Osinbajo
Maiyashi yace an kammala rijistan an majalisan kuma an bashi katin zama mamba a jam’iyyar.
A ranar Lahadi ne Sani ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar APC mai mulki.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar Progressive Congress (APC), babin jihar Delta a ranar Talata, 23 ga watan Oktoba ta rasa wani babban jigonta uma mai dauke mata nauyin bukatun ta da ya shafi kudi.
Jigon ya sauya sheka ne zuwa babbar jam’iyyar adawar kasar wato Peoples Democracy Party (PDP).
Mai sauya shekar, Cif Emmanuel Ogwuda wanda ya sanar da sauya shekar nasa a Asaba, babar birnin jihar ya bayyana cewa APC bata da nagartaccen tsari na shugabanci da zai daure kan damokardiyya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng