APC ta sake shiga matsala bayan wani babban jigonta ya koma PDP a Delta

APC ta sake shiga matsala bayan wani babban jigonta ya koma PDP a Delta

Jam’iyyar Progressive Congress (APC), babin jihar Delta aranar Talata, 23 ga watan Oktoba ta rasa wani babban jigonta uma mai dauke mata nauyin bukatun ta da ya shafi kudi.

Jigon ya sauya sheka ne zuwa babbar jam’iyyar adawar kasar wato Peoples Democracy Party (PDP).

Mai sauya shekar, Cif Emmanuel Ogwuda wanda ya sanar da sauya shekar nasa a Asaba, babar birnin jihar ya bayyana cewa APC bata da nagartaccen tsari na shugabanci da zai daure kan damokardiyya.

APC ta sake shiga matsala bayan wani babban jigonta ya koma PDP a Delta
APC ta sake shiga matsala bayan wani babban jigonta ya koma PDP a Delta
Asali: Depositphotos

A cewarsa, sauya shekarsa daga APC ya zama dole domin ya bayar da damar samun ci gaba ga mutanensa inda ya bayana cewa PDP ce kadai zata iya tabbatar da hakan.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu cin hanci da rashawa ne babban matsalarmu - Osinbajo

Yayi zargin cewa mutun daya ne ke janye da ragamar APC wanda a cewarsa hakan ya sabama ka’idar mulkin damokradiyya wanda ya ba kowani dan jamiyya yanci.

Ya kuma bayyana cewa jihar ta samu gagarumin ci gaba a karashin gwanatin Ifeanyi Okowa wato gwamnan jihar wanda ya kasance dan PDP.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng