Nigeria: Buhari, Sultan na daga cikin musulmai 50 mafi shahara a duniya

Nigeria: Buhari, Sultan na daga cikin musulmai 50 mafi shahara a duniya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, sun kasance daga cikin jerin Musulmi 50 mafi daukaka a duniya

- Rahoton jadawalin sunayen, wanda aka fara wallafa shi a 2009, na samun kyakkyawan bincike daga cibiyar tsare tsaren Musulunci RISC da ke Amman, kasar Jordan

- Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogon ne ya kasance na daya a jerin sunayen Musulmi mafi daukaka a duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sarkin Musulmi, kuma shugaban majalisar harkokin addinin Musulunci ta kasa NSCIA, Muhammadu Sa'ad Abubakar, sun kasance daga cikin 'yan Nigeria, da suka samu shiga cikin jerin Musulmi 50 mafi daukaka a duniya.

An saka sunayen nasu ne a wani rahoton shekara shekara da ake fitarwa karo na 10 mai taken: "Musulmai 500: Musulmai 500 mafi daukaka a duniya" zango na 2019.

Rahoton jadawalin sunayen, wanda aka fara wallafa shi a 2009, na samun kyakkyawan bincike da tattara bayanai daga cibiyar tsare tsaren Musulunci RISC da ke Amman, kasar Jordan.

Rahoton ya bayyana cewa, ba wai kasancewarka dan kasa kawai ke sa a dauke ka ba, wadanda aka zaba suna taka muhimmiyar rawa a cikin al'ummar Musulmi a fadin duniyar.

KARANTA WANNAN: Imo: Mata da matasa sun yi zanga zangar nuna adawa ga Oshiomhole, sun bukaci a tsige shi

Nigeria: Buhari, Sultan na daga cikin musulmai 50 mafi shahara a duniya
Nigeria: Buhari, Sultan na daga cikin musulmai 50 mafi shahara a duniya
Asali: Twitter

Daga cikin ka'idojin da ake dubawa yayin daukar sunayen, akwai; mutumin da ke rike da wani mukami (walau na al'ada, arziki, siyasa, baiwa, da dai sauransu), da za su iya kawo wani babban sauyi a rayuwar Musulmai da Musulunci a fadin duniyar.

A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance na 17 a jerin sunayen (wanda yake na 19 a shekarar 2017, na 24 a 2016), shi kuma Sultan wanda ya kasance na 16 a 2009, yanzu kuma ya zama na 21 a wannan shekarar, (a 2016 shi ne na 24, ya dawo na 23 a shekarar data gabata).

Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogon ne ya kasance na daya a jerin sunayen Musulmi mafi daukaka a duniya, bayan da ya haura daga na 5 a shekarar 2017, don maye gurfin Farfesa Sheik Ahmad Muhammad At-Tayyeb, babbab Shehin jami'ar Al-Azhar kuma babban limamamin masallacin Al-Azhar da ke kasar Masar.

DUBA WANNAN: Yadda mutane 5,000 suka fice daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar Akwa Ibom

Sarki Salman Abdul-Aziz Al-Saud na kasar Saudi Arabia, ya samu damar ci gaba da kasancewa na biyu a jerin sunayen kamar yadda yake a shekarar 2017, wanda kuma ya tilastawa Sarki Abdullah Al-Hussein na kasar Jordan ci gaba da zama na Uku. Sarkin Jordan shi ne na daya a 2016.

Babban alkalin alkalai na kotun kolin kasar Iran, Ayatollah Hajj Sayyid Ali Khamenei ya kasance na 4, yayin da Sarki Mohammed VI, na kasar Morocco ya kasance na biyar.

KARANTA WANNAN: Malaman addinai na zuwa wajen Buhari don daukar hoto ba don yi masa wa'azi ba - Dr. Bakare

Babban dan wasan taka leda na kasar Masar, Mohammed Salah, ya kasance na 45, inda kuma babban Malamin addinin Musulunci na garin Maiduguri, Sheik Ibrahim Salih, ya sauko daga na 50 a 2017 zuwa na 59 a wannan shekarar.

Wasu daga cikin 'yan Nigeria da aka sanya sunayen nasu a cikin jerin Musulmi 500 mafi shahara a duniya, sun hada da Dr. Ibrahim Datti Ahmed; shugaban mabiya akidar Shi'a Sheikh Ibraheem Zakzaky; Babban limamin kungiyar Ansar-Ud-Deen, Dr. Abdrahman Olanrewaju Ahmad; Prince Bola Ajibola; Imam Muhammad Ashafa; Sheikh Tahir Usman Bauchi; Alhaji Aliko Dangote; Sheikh Yakubu Musa Katsina; Farfesa Ishaq Olanrewaju Oloyede da kuma shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, da dai sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel