Malaman addinai na zuwa wajen Buhari don daukar hoto ba don yi masa wa'azi ba - Dr. Bakare
- Dr. Tunde Bakare, ya ce ya zamarwa yan Nigeria su kasance masu fadin gaskiya komai dacinta, idan har aka zo kan batun mulki
- Bakare, ya caccaki shuwagabannin addinai, wadanda ya zarga da gaza fayyacewa shugaban kasa Buhari halin da jama'a suke ciki
- Ya zargi malaman addinai da zuwa wajen Buhari don daukar hoto da shi kawao ba wai don ci gaban al'umma ba
Babban malamin majami'ar Latter Rain Assembly, Dr. Tunde Bakare, ya ce ya zamarwa yan Nigeria su kasance masu fadin gaskiya komai dacinta, idan har aka zo kan batun mulki, tare da kuma ajiye abun ya kira 'Al'adar munafurci a siyasa'.
Bakare, ya caccaki shuwagabannin addinai, wadanda ya zarga da gaza amfani da damar da suka samu ta ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, don fayyace masa gaskiyar halin da jama'a suke ciki, da yi masa wa'azi musamman kan mawuyacin halin da yan siyasar kasar suka jefa al'umma a ciki.
Bakare ya bayyana hakan a jiya Lahadi a wani taron godiya ga Ubangiji, da aka gudanar don murnar cikar babbar cocin Foursquare Gospel Church shekaru 16 da kafuwa a Asokoro, babban birnin tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN: Dan shekara 85 ya lashe zaben kasar Kamaru karo na 7

Asali: Depositphotos
Ya ce, "Ku kalli yadda kasar take ciki; ku kalli wadanda ke nuna su na Allah ne; ku kalli yadda wasu ke handamar dukiyar al'umma saboda matakin da suke da shi a cikin gwamnati. Sun manta da cewa Allah ne ya kaisu matsayin da suke yanzu, kuma yana da hanyoyin tsigesu daga matsayin.
"Lokacin sa Samuel (a cikin Bible) ya shiga birninsu, sarkin ya tashi da rawar jiki, amma a lokacin da wasu malaman majami'u suka shuga fadar shugaban kasa, sai gashi sune suke rawar jiki. Abunda kawai suke so shine su dauki hoto da shugaban kasa," a cewarsa.
Ya yi nuni da cewa kasar ta dade tana fuskantar cin fuskar cikin gida sakamakon yadda wasu a kasar ke kallon kansu a matsayin mafifita akan sauran jama'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng