Ana-wata-ga-wata: Hukumar EFCC ta bankado wani gidan alfarma na tsohon gwamnan Ekiti, Fayose
- EFCC ta bankado wani gidan alfarma na tsohon gwamnan Ekiti, Fayose
- Har yanzu dai Fayose na a hannun EFCC tsare
- Ana tuhumar sa da laifukan almundahana
Yayin da hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa tu'annati ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance ke ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ta saki wasu sabbin bayanan da ba'a sani ba game da shi.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yabawa Cif Obasanjo
Hukumar dai ta saki hotunan wani makeken gidan alfarma mai tsadar gaske da suka ce na tsohon gwamnan ne kuma suna zargin da kudin haram ne ya samu gidan a lokacin da yake gwamna.
Gidajen dai da suke zargin na tsohon gwamnan ne sun ce suna a garin Abuja ne, babban birnin tarayya da kuma jihar Legas.
Yanzu haka dai gwamnan na tsare a hedikwatar hukumar ta EFCC ne inda yake ansa tambayoyin da suka jibanci yadda ya tafiyar da gwamnatin sa a lokacin yana gwamna.
A wani labarin kuma, Kungiyar matan sojojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force Officers' Wives Association (NAFOWA) sun koyar da akalla matasa da kuma matan sojojin da suka mutu su 100 sana'oin hannu domin dogaro da kai na garin Kaiji.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng