Yanzu-Yanzu: Sanata Magnus Abe ya yi tsokaci game da batun ficewar sa daga jam'iyyar APC
- Sanata Magnus Abe ya yi tsokaci game da batun ficewar sa daga jam'iyyar APC
- Yace shi yana nan a APC daram dam
- Sanatan dai suna takun saka ne da Ministan sufuri Rotimi Amaechi
Sanata Magnus Abe dake zaman dan majalisar dattawan dake wakiltar mazabar jihar Ribas ta gabas ya yi tsokaci game da labarin da ke yawo na cewa wai ya fita daga jam'iyyar APC mai mulki a ranar Asabar.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Wani tsohon babban Jami'in gwamnatin tarayya a rasu
Da yake zantawa da wakilin majiyar mu a garin Abuja, babban birnin tarayya, Sanata Abe ya karyata batun inda yace labarin kanzon kurege ne kawai amma shi har yanzu yana jam'iyyar APC mai mulki.
Legit.ng Hausa ta samu cewa an jima dai ana takun saka a tsakanin bangarorin jam'iyyar biyu a jihar ta Ribas inda wasu ke goyon bayan ministan Sufuri kuma tsohon gwamnan jihar ta Ribas, Rotimi Amaechi yayin da wasu kuma ke goyon bayan shi Sanata Abe din.
Haka zalika gaba daya ma dai jam'iyyar ta APC na fuskantar kalu-bale da yawa a jahohi da dama biyo bayan korafe-korafen zabukan fitar da gwanin da aka yi satittikan da suka shude.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng