Zan sanar da sabuwar jam'iyyar da na koma, kuma zan yi takara a 2019 - Shehu Sani

Zan sanar da sabuwar jam'iyyar da na koma, kuma zan yi takara a 2019 - Shehu Sani

Jim kadan bayan murabus dinsa daga jam'iyyar All Progressives Congress APC, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa lallai fa zai yi takara a zaben 2019 amma a wata jam'iyyar daban.

Sanatan ya sanar da hakan ne a wata jawabi da ya sakai da daddaren nan bayan bayyana banbancinsa da wadanda suka sauya sheka gabaninsa.

Yace: "Sako zuwa ga Alumman Kaduna ta tsakiya da Jihar Kaduna baki daya;A yau 20/102018 na fiche daga cikin Jamiyar APC.Nan Bada dadewa ba,zan Sanar daku Jamiyar Da zan koma da magoya baya na.Kuma zamu yi kira da kuma kuyi haka. Ina kara tabbatar maku da cewa zan tsaya takara kuma zaa hadu a final kaman inda nayi alkawari Insha Allah.Da ikon Allah zamu kubutad da talakawan Kaduna daga Halin Da suka Sami kansu a ciki Insha Allah."

Mun kawo muku rahoton cewa Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Dan majalisar ya dauki wannan matakin ne sakamakon rikice-rikicen da suka rika faruwa gabanin gudanar da zaben cikin gida a jam'iyyar ta APC a mazabar Kaduna ta Tsakiya.

Rahotanni sun bayyana cewar mai bawa gwamna shawara a kan harkokin siyasa, Malam Uba Sani shine wanda jam'iyyar ta mika sunansa a matsayin dan takarar kujerar Sanata na yankin Kaduna ta Tsakiya.

Shehu Sani ya aike da wasikar murabus dinsa ne zuwa ga ciyaman din jam'iyyar na Ward 6 da ke Tudun Wada a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel