Buhari, Atiku sun yi Allah-wadai da rikicin Kasuwar Magani da ya salwantar da rayuka 55
- Buhari da Atiku, sun yi Allah-wadai da rikicin da ya barke a Kasuwan Magani a jihar Kaduna, wanda ya lakume rayuwaka 55
- A cewar shugaba Buhari, wanzar da zaman lafiya shine babban mataki na ci gaban kowacce al'umma
- Atiku ya ce suna nan suna jiran irin kokarin da za ayi don tabbatar da hukunci ga wadanda aka kama da sa hannu a tayar da husumar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Alhaji Atiku Abubakar, sun yi Allah-wadai da rikicin da ya barke a Kasuwan Magani a jihar Kaduna, wanda kuma ya lakume rayukan akalla mutane 55.
Da yake tsokaci kan rikicin, shugaban kasa Buhari ya ce yawaitar rikice rikicen da ke janyo salwantar rayukan sakamakon sabani na fahimta, da ya kamata a magance shi ne ta hanyar zama a teburin sasanci, ya kuma bayyana hakan a matsayin lamari mai matukar sanya damuwa.
Jawabin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa, daga mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu, da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A cewar shugaban kasar, "Babu wani addini ko kabila da zata amince da wannan kisan kiyashin da ake yiwa rayukan jama'a," yana mai cewa "wanzar da zaman lafiya shine babban mataki na ci gaban kowacce al'umma."
KARANTA WANNAN: Daga karshe: Shehu Sani ya fayyace dalilin ficewarsa daga jam'iyyar APC

Asali: Facebook
Ya yi nuni da cewa, ma damar aka ce babu hadin kai da zaman lafiya a tsakanin jama'a, to kuwa babu ta yadda za a samu kyakkyawan muhallin da za a rinka gudanar da hada hadar yau da kullum ta kasuwanci.
Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa: "Rikici ba zai taba zama abokin zaman lafiya ba. A bangare daya kuwa, hakikance da tashin hankula, shi ke tarwatsa rayuwar mutane. Rikici kamar wata annoba ce da ke zuwa da mummunan sakamako ga kowa. Hakika, yarda da zaman lafiya, da kuma amince da zaman lafiyar, ya zama tilas, don shine mafita."
A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana nasa takaicin kan wannan rikici na Kasuwan Magani a Kaduna, shima tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasar karkashin PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da wannan rikici.
Da ya ke bayyana alhininsa kan asarar rayukan da aka yi, Atiku ya ce: "Hakika na kadu matuka da asarar rayukan da aka yi, biyo bayan rikicin da ya barke a Kasuwan Magani, jihar Kaduna, a irin salon da ya zamar mana kamar ruwan dare a kasar."
"Ina rokon Allah ya gafartawa wadanda rayukansu suka salwanta, yayin da kuma muke jiran muga irin kokarin da za ayi don tabbatar da hukunci ga wadanda aka kama da sa hannu a tayar da husumar," a cewar Atiku.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng