Da dumi dumi: Sanata Dino Melaye ya amayar da ta cikinsa kan ficewar Shehu Sani daga APC

Da dumi dumi: Sanata Dino Melaye ya amayar da ta cikinsa kan ficewar Shehu Sani daga APC

- Sanata Dino Melaye, ya tofa albarkacin bakinsa kan ficewar Sanata Shehu Sani daga jam'iyya mai mulki ta APC

- Sanatan wanda ya jajantawa Shehu Sani kan hakan, ya kuma godewa Allah da ya sa bai kasance karen farauta a hannun jam'iyyar APC ba

- A safiyar yau ne dai Shehu Sani ya aike da wasikar murabus dinsa zuwa ga ciyaman din jam'iyyar na Ward 6 da ke Tudun Wada a Kaduna

A ranar asabar dinnan ne Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya tofa albarkacin bakinsa kan ficewar Sanata Shehu Sani daga jam'iyya mai mulki ta APC.

Dino Melaye, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter, ya ce: "Sanata Shehu Sani ya fice daga jam'iyyar APC. Mutanen da suka nuna maka kiyayyarsu da safe har da yamma, wai sune za su zo suna ikirarin sonka da daddare, ya kamata dai mu hankalta.

"Na gode maka Ubangiji na sa ka sa ban zama karen farauta a jannun jam'iyyar 'biya kudi ka dauka' ba (APC). In jajanta maka abokina."

KARANTA WANNAN: Wata sabuwa: Muna da dalilan gurfanar da Adeleke amma bamu da na Adeosun - Rundunar 'yan Sanda

Da dumi dumi: Sanata Dino Melaye ya amayar da ta cikinsa kan ficewar Shehu Sani daga APC
Da dumi dumi: Sanata Dino Melaye ya amayar da ta cikinsa kan ficewar Shehu Sani daga APC
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Dan majalisar ya dauki wannan matakin ne sakamakon rikice-rikicen da suka rika faruwa gabanin gudanar da zaben cikin gida a jam'iyyar ta APC a mazabar Kaduna ta Tsakiya.

Rahotanni sun bayyana cewar mai bawa gwamna shawara a kan harkokin siyasa, Malam Uba Sani shine wanda jam'iyyar ta mika sunansa a matsayin dan takarar kujerar Sanata na yankin Kaduna ta Tsakiya.

Shehu Sani ya aike da wasikar murabus dinsa ne zuwa ga ciyaman din jam'iyyar na Ward 6 da ke Tudun Wada a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng