An gargadi sojojin saman Najeriya da su kiyayi neman 'yan matan kabilar Agatu
- An gargadi sojojin saman Najeriya da su kiyayi neman 'yan matan kabilar Agatu
- Shugabar karamar hukumar Agatu ce ta yi wannan kashedin
- Tace 'yan matan na da dafi a jikin su
Comfort Alhassan dake zaman shugabar karamar hukumar Agatu ta gargadi jami'an sojojin saman Najeriya da aka tura aikin tabbatar da zaman lafiya da su guji bin 'yan matan karamar hukumar don gudun fadawa cikin wani mawuyacin hali.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Jerin sunayen mutane 46 da za su kara da Buhari a 2019
Shugaban karamar hukumar dai ta ce su 'yan matan na karamar hukumar suna da wani dafa'i a tare da su wanda kan bi mutum ya lalata masa rayuwa idan dai har ya fara kwanciya da su kuma bai aure su ba.
Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa Comfort Alhassan din ta kara da cewa ta san cewar su mazan ba katakai bane za su iya jin sha'awar neman matan to amma tana shawartar su da su fara zuwa su nemi izini a wurin iyayen su kafin nan.
Daga karshe kuma ta yabawa gwamnatin tarayya da ta kafa sansanin sojin da nufin tabbatar da zaman lafiya dawwamamme a karamar hukumar da ma sauran yankunan su makwafta.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng