Barazanar gwamnati na 'ba aiki ba biyan albashi' ba zata hanamu zuwa yajin aiki ba - COEASU

Barazanar gwamnati na 'ba aiki ba biyan albashi' ba zata hanamu zuwa yajin aiki ba - COEASU

- Kungiyar malaman kwalejojin ilimi, COEASU, ta ce ko kadan ba zata razana daga barazanar gwamnatin tarayya na tsarin 'ba aiki ba biyan albashi' ba

- Shugaban kungiyar ya bayyana tsarin gwamnatin a matsayin tsantsar rashin darajta ma'aikata, da kuma rashin martabar bukatun aikin gwamnati

- A cewar sa, tsawon shekaru kenan malamai a kwalejojin ilimi suke fuskantar ragin albashi ba tare da sanin wani kwakkwaran dalili ba

Kungiyar malaman kwalejojin ilimi, COEASU, ta ce ko kadan ba zata razana daga barazanar gwamnatin tarayya na tsarin 'ba aiki ba biyan albashi' da ta bullo da shi ba. Shugaban kungiyar na kasa, Nuhu Ogirima ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, yana mai kiran mambobin kungiyar da su kasance a cikin zaman shirin ko-ta-kwana.

"Kamar yadda muka kammala kashin farko na yajin aikin da muka shiga, muna kiran mambobin kungiyarmu da kada su razana da tsarin gwamnati na 'ba aiki ba biyan albashi'. Illa ma dai muna fatan wannan barazanar ta kara mana kwarin guiwa na nuna masu cewa 'tura fa ta kai bango'.

"Tunda dai gwamnati ta ce "Ba aiki ba biyan albashi,' to muna so kowa ya shirya, don kuwa akwai babbar badakala a nan gaba, domin ba zamu ja da baya ba, kasancewar idan har muka dakata daga wannan yunkuri namu, to tabbas babu ranar da za'a cika mana bukatunmu"

KARANTA WANNAN: Madallah: Gwamnoni sun goyi bayan sharadin da Buhari ya gindaya kafin bayar da kudin Paris Club

Barazanar gwamnati na 'ba aiki ba biyan albashi' ba zata hanamu zuwa yajin aiki ba - COEASU
Barazanar gwamnati na 'ba aiki ba biyan albashi' ba zata hanamu zuwa yajin aiki ba - COEASU
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar ya bayyana tsarin gwamnatin na 'ba aiki ba biyan albashi' a matsayin tsantsar rashin darajta ma'aikata, da kuma rashin martabar bukatun aikin gwamnati, da kaucewa dokokin da aikin gwamnati a kasar ya tanadar.

A cewar sa, tsawon shekaru kenan malamai a kwalejojin ilimi suke fuskantar ragin albashi da kuma cire wani kaso daga cikin albashin nasu ba tare da sanin wani kwakkwaran dalili ba, musamman ma na rashin aikwatar da PAA.

Ya yi nuni da cewa babu wani yunkuri da gwamnatin tayi na kara yiyuwar kara masu albashi duk da cewa farashin mai na ci gaba da hauhauwa, yana mai cewa "ba a taba kaimu makura ba kamar yanzu, wannan ya nuna tsantsar gazawar gwamnati mai ci a yanzu, ya zama wajibi na fadi hakan."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng