Da dumi-dumi: An gano inda shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya ke buya (Hotuna da Bidiyo)

Da dumi-dumi: An gano inda shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya ke buya (Hotuna da Bidiyo)

Bayan watanni da masu yawa ta bacewarsa, an gano shugaban haramtaciyar kungiyar masu fafutikan neman kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kani a birnin Jerusalem da ke kasar Isra'ila a yau 19 ga watan Oktoban 2018.

Hotuna da bidiyon Nnamdi Kanu yana bauta a Jerusalem sun karade kafafen sada zumunta bayan Radio Biafra da wallafa hotunan da bidiyon.

Kanu dai ya bace ne a watan Satumban 2017 bayan sojojin Rundunar Phython Dance sun kai wata farmaki gidansa.

An gano ashe Nnamdi Kanu yana Jerusalem (Hotuna da Bidiyo)
An gano ashe Nnamdi Kanu yana Jerusalem (Hotuna da Bidiyo)
Asali: Facebook

Bayan bacewarsa mutane da kungiyoyi daban-daban suna ta korafi cewar gwamnatin tarayya ne da boye shi amma kuma babu wata hujja da ke nuna hakan.

Wasu kuma na ganin ya tsere ne saboda haramcin da gwamnati ta yiwa kungiyar nasa bayan an ambata kungiyar a matsayin kugiyar ta'addanci.

An gano ashe Nnamdi Kanu yana Jerusalem (Hotuna da Bidiyo)
An gano ashe Nnamdi Kanu yana Jerusalem (Hotuna da Bidiyo)
Asali: Twitter

Ga dai biyon a kasa:

Nnamdi Kanu da 'yan kungiyarsa sun sha yiwa gwamnati barazanar cewa za su tayar da hankalin al'umma kuma su hana a gudanar da zabe a wasu jihohin kudu muddin gwamnatin tarayya ba ta amince da ba su ikon kafa kasarsu ba.

Ga wai hotuna da bidiyonsa a kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel