Al'ummar Musulmi a jihar Ekiti sun fara caccakar Fayemi kan nuna wariya wajen nadin mukamai

Al'ummar Musulmi a jihar Ekiti sun fara caccakar Fayemi kan nuna wariya wajen nadin mukamai

- Al'ummar Musulmi a jihar Ekiti, sun yi Allah-wadai da wasu mukamai 3 da gwamnan jihar Kayode Fayemi yayi

- Sun bayyana wannan nadin mukamai na sabon gwamnan a matsayin hanyar nuna tsantsar kiyayya da wariyarsa ga al'ummar Musulmi a jihar

- Kungiyar ta yi kira ga gwamnan da ya gaggauta sake fasalin wannan nadin mukaman, tare da sanya Musulmai a ciki don suma susan ana yi da su

A ranar Alhamis, Al'ummar Musulmi a jihar Ekiti, sun yi Allah-wadai da wasu mukamai 3 da gwamnan jihar Kayode Fayemi yayi, bayan hawansa kujerar gwamnan jihar.

Tajudeen Ahmed, kodinetan kungiyar matasa musulmi ta kasa (NACOMYO), ya bayyana wannan rashin jin dadin nasu a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan da suka gudanar da zanga zangar luma a babban masallancin juma'a na Ado Ekiti.

Ya bayyana wannan nadin mukamai na sabon gwamnan, Fayemi, a matsayin "hanyar nuna tsantsar kiyayya da wariyarsa ga al'ummar Musulmi a jihar".

KARANTA WANNAN: Mansur Dan-Ali: Jam'iyyun hamayya na tanadar makamai don amfani dasu a zaben 2019

Tajudeen Ahmed ya ce nadin mukaman sakataren gwamnatin jihar, shugaban ma'aikata da kuma babban sakataren watsa labarai ya saba da yin dai-daito da kuma adalci ga al'ummar Musulmi kamar yadda Fayemi ya yi alkawari a lokacin yakin zabensa.

Al'ummar Musulmi a jihar Ekiti sun fara caccakar Fayemi kan nuna wariya wajen nadin mukamai
Al'ummar Musulmi a jihar Ekiti sun fara caccakar Fayemi kan nuna wariya wajen nadin mukamai
Asali: Depositphotos

"Rashin sanya wani Musulmi a cikin manyan mukaman gwamnatin jihar abun damuwa ne matuka, kuma rashin adalci ne, wanda ba zamu aminta da shi ba," a cewar Ahmed.

"Al'ummar Musulmi a Ekiti sun ga yadda nadin mukaman ya kasance, wannan kuwa alamace karara ta cewar gwamnan na yunkurin mayar da Musulmi saniyar ware a cikin gwamnatin tasa, da kuma cire dukkanin musulmai daga wasu manyan bangarorin mukamai."

Kungiyar ta ce Musulmai na da kaso 40 na adadin mazauna jihar Ekiti, tana mai karawa da fadin cewa sun baiwa gwamnan duk wani goyon baya da yake bukata a lokacin da aka gudanar da zaben gwamnan jihar, wanda ya bashi nasara.

KARANTA WANNAN: Atiku Abubakar: Zan tabbata na yiwa Buhari ritaya a siyasa don ya koma Daura a 2019

A cewar Ahmed, rashin sanya Musulmai a cikin nadin mukaman gwamnatin, ya sabawa dokoki da tsare tsaren gwamnatin jihar kamar yadda yake kunshe cikin kundin mulkin kasa na 1999 (kamar yadda aka sabunta shi).

Kungiyar ta yi kira ga gwamnan da ya gaggauta sake fasalin wannan nadin mukaman da yayi, tare da sanya Musulmai a ciki don suma susan ana yi da su ba wai a nuna wariya a garesu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng