Mansur Dan-Ali: Jam'iyyun hamayya na tanadar makamai don amfani dasu a zaben 2019

Mansur Dan-Ali: Jam'iyyun hamayya na tanadar makamai don amfani dasu a zaben 2019

- A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta zargi jam'iyyun hamayya da tara makamai don tayar da zaune tsaye a babban zaben 2019

- Haka zalika ta yi zargin cewa jam'iyyar hamayyar na kokarin tayar da rikicin kabilanci don gurgunta APC a zaben mai zuwa

- An samar da matsaya ta tura jami'an tsaro a gaba daya jihohin, da nufin dakile duk wani tashin hankali yayin gudanar da zaben

A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta yi zargin cewa jam'iyyun hamayya sun dukufa wajen tara makamai don tayar da zaune tsaye a babban zabe na 2019 da ke gabatowa. Haka zalika ta yi zargin cewa jam'iyyar hamayyar na kokarin tayar da rikicin kabilanci don gurgunta APC a zaben mai zuwa.

Mansur Dan-Ali, ministan tsaro, ya yi wannan zargin jim kadan bayan kammala taron shuwagabannin tsaro na kasa da ya gudana a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci taron, sun hada da ministan tsaro, Mansur Dan Ali; babban mai bada shawara kan sha'anin tsaro na kasa, Babangana Monguno; hafsan rundunar sojin kasa, Lt.-Gen. Tukur Buratai; shugaban rundunar sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; shugaban runduanr sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, da kuma sifeta janar na rundunar 'yan sanda, Ibrahim Idris.

KARANTA WANNAN: Atiku Abubakar: Zan tabbata na yiwa Buhari ritaya a siyasa don ya koma Daura a 2019

Mansur Dan-Ali: Jam'iyyun hamayya na tanadar makamai don amfani dasu a zaben 2019
Mansur Dan-Ali: Jam'iyyun hamayya na tanadar makamai don amfani dasu a zaben 2019
Asali: Facebook

Dan-Ali ya shaidawa manema labarai cewa: "Taron ya fara da tattaunawa kan sha'anin tsaro gaba daya, da kuma duba batun tsaron a fuskar babban zabe na 2019 da ke gabatowa don samar da hanyoyin tabbatar da zaman lafiya kafin zaben, dama bayan kammala shi.

"An samar da matsaya ta tura jami'an tsaro a gaba daya jihohin, da nufin dakile duk wani tashin hankali yayin gudanar da zaben, da kuma yunkuri da jam'iyyun siyasa za suyi na tayar da zaune tsaye.

"Haka zalika a taron, an tattauna kan hanyoyin da za abi, a wani yunkuri na wasu ke yi na matsin lamba ga hukumar gudanar da zabe don cimma wasu manufofi nasu ta hanyar amfani da jami'an tsaro, wajen dakile ire iren wadannan mutane daga satar kayan zabe.

KARANTA WANNAN: Wasika ta musamman daga babban Editan jaridar Legit.ng (tsohuwar jaridar NAIJ.com)

"Babban bangaren da muka mayar da hankali shine tashin hankula da ake samu gabanin zabe, akwai 'yan siyasa masu ci da zuci, da ka iya kirkiro rikicin kabilanci ko na addini don raba kawunan jama'a tare da tayar da zaune tsaye a kasar.

"Haka zalike, akwai abun damuwa matuka, kan yadda wasu jam'iyyun hamayya ke tara makanai don baiwa yan bangar siyasa da nufin daukar doka a hannunsu da zaran sun samu damar yin hakan," a cewar Mansur Dan-Ali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng