Matsalolin Wutar Lantarki ba za su gyaru da Siddabaru ba - Fashola

Matsalolin Wutar Lantarki ba za su gyaru da Siddabaru ba - Fashola

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa, Ministan makamashi, ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Fashola, ya bayyana cewa kwanci tashi matsalolin wutar lantarki da kasar nan ta Najeriya ke fuskanta za su zamto tarihi ba dade ko ba jima.

Ministan ya bayyana cewa, a yayin da kwanci tashi ingancin wutar lantar ke kara habaka a kasar nan a kullum, sai dai ba za a iya magance wannan matsala da wani sihiri ko siddabaru cikin dare daya tamkar wata walkiya ko kiftawar idanu.

Dangane da binciken manema labarai a ma'aikatar makamashi, kididdiga ta alkalumma ta bayyana cewa, karfin wutar lantarki na kasar nan yana kan ma'aunin MegaWatts 3,729 a ranar Larabar da ta gabata.

Matsalolin Wutar Lantarki ba za su gyaru da Siddabaru ba - Fashola
Matsalolin Wutar Lantarki ba za su gyaru da Siddabaru ba - Fashola
Asali: Depositphotos

Fashola wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis yayin kaddamar da wasu sabbin aikace-aikace a tashar makamashi ta Ejigbo dake jihar Legas, ya yabawa babban kamfanin raba wutar lantarki na Najeriya dangane da rawar da yake ci gaba da takawa ta inganta wutar lantarki a fadin kasar nan.

Mista Fashola ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da tsayuwar dakansa a kan inganta makamashin wutar lantarki fadin kasar nan duk da tabarbarewar da tayi a sakamakon rikon sakainar kashi na gwamnatocin baya.

KARANTA KUMA: Gwamnoni za su sanya dokar ta baci kan harkar ilimi a jihohin su

Kamar yadda Ministan ya bayyana Jaridar LEGIT.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu akwai kimanin manyan aikace-aikace 90 da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a fadin kasar nan domin inganta nagarta ta wutar lantarki.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, a jiya Alhamis shugaban kasa Buhari ya gudanar da wata muhimmiyar ganawa da shugabannin tsaro na kasa a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng