Shugaban kasa ya ba Mata mukaman Ministoci masu gwabi a Ehiopia

Shugaban kasa ya ba Mata mukaman Ministoci masu gwabi a Ehiopia

Labari ya zo mana daga gidan yada labarai na BBC cewa Mata ne su ka tashi da rabin mukaman da aka bada na Minista a Kasar Ethiopia. Daga ciki kuma har da manyan Ministoci da ake ji da su a Kasar.

Shugaban kasa ya ba Mata mukaman Ministoci masu gwabi a Ehiopia
A Ethiopia akwai wakilcin jinsi daidai a majalisar tsakanin mata da maza
Asali: UGC

Shugaban Kasar Habasha Firayim Minista Abiy Ahmed ya zabi Mace a matsayin Ministar tsaro na Kasar a sauye-sauyen da aka yi a Gwamnatin sa. Ministan dai ya nuna cewa Mata sun fi rikon amana da rashin handama a mulki.

Wani babban Jami’in Majalisar UN daga Kasar ne ya fitar da sunayen sababbin Ministocin da aka nada a shafin sa na Tuwita. Yanzu dai wata Baiwar Allah mai suna Aisha Mohammed ce ta zama ministar tsaron kasar a karon farko.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya jinjinawa abin da Jonathan yayi bayan zaben 2015

Abiy wanda ya hau mulki kusan wata shida da su ka wuce ya kuma rage yawan Ma’aikatun Kasar inda ya zaftare adadin Ministocin sa daga 28 zuwa 20 kacal. Tsohuwar Shugabar Majalisa Muferiat Kamil tana cikin sababbin Ministocin.

Yanzu dai Shugaban kasar mai shekaru 42 wanda ya gaji Hailemariam Desalegn yana cigaba da kawo gyara a kasar ta Afrika inda yace Mata za su rike bakin aikin su da kyau tare da kawo zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng