Zaben 2019: Manjo Al-Mustapha yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

Zaben 2019: Manjo Al-Mustapha yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

Tsohon dogari ga tsohon shugaban kasar Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayi alkawarin maido da kasar nan akan turba madaidaiciya idan dai har aka zabe shi shugaban kasa a zaben 2019.

Manjo Al-Mustapha da ke zaman dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PPN ya shaidawa manema labarai a garin Abuja cewar idan har ya zama shugaban kasa to tabbas zai yi kokari wajen ganin ya gyara tabarbarewar da harkokin sukayi a wannan mulkin na Shugaba Buhari.

Zaben 2019: Manjo Al-Mustapha yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo
Zaben 2019: Manjo Al-Mustapha yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo
Asali: UGC

KU KARANTA: Ka sauka daga mukamin ka - Akpabio ya shaidawa Saraki

Haka zalika ya bayyana cewa yan kasar sun cancanci kyakkyawan shugabanci a dukkan matakai shi yasa ma ya ga ya dace ya fito takarar domin ya cece su daga kangin mugun shugabancin da suke ciki.

Da yake bayani game da dan takarar, shugaban jam'iyyar ta PPN, Honorabul Eyiowuawi Razak ya kwatanta Manjo Al-Mustapha a matsayin babban mai kishin kasa da ya sadaukar da rayuwar sa wajen cigaban ta.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya shaidawa manema labarai cewa mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bashi tabbacin cewa gwamnatin tarayya bata da shirin sayar da kamfanin nan na mulmula karafa na Ajaokuta da ke a jihar ta Kogi.

Gwamnan ya yi wannan karin hasken ne lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wani taron sirri da mataimakin shugaban kasar a fadar mulki ta AsoRock, Abuja, babban birnin tarayya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel