Wata sabuwa: An yi wa baitul malin Najeriya kar-kaf cikin kwanaki 13 da suka gabata
Alkaluman da muke samu daga babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) na nuni ne da cewa baitul malin kasar nan yayi kasa sosai da bai taba yi ba a cikin kusan watanni bakwai da suka shude inda ya rage da sama da Dalar Amurka biliyan 1 cikin kwanaki 13 kacal.
Kamar yadda muka samu, asusun na ajiyar kudaden waje na kasar akwai Dalar Amurka biliyan 44.30 a ranar 28 ga watan Satumba da ta gabata amma kuma a ranar 2 ga watan Oktoba akwai Dalar Amurka biliyan 44.02.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Ba tsoron ciki: Wani dan luwadi ya fadi dalilin sa na neman maza
Haka zalika mun samu cewa daga 2 ga watan Oktoba din zuwa 15 ga watan na Oktoba asusun ajiyar na kudaden kasar wajen na Najeriya babu komai sai Dalar Amurka biliyan 43.
Baitul malin kasar dai yana kasa yana sama ne a 'yan shekarun nan tun bayan da farashin danyen mai yai faduwar toto a ruwa wanda kuma da shi ne kasar ke takama.
A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta saki alkaluman ta na kasafin kudin shekarar 2019 mai zuwa inda ta fitar da Naira tiriliyan 8.6.
Wannan adadin kudin dai idan aka dube su sun yi kasa da kasafin kudin na shekarar da ta gabata na Naira tiriliyan 9.1.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng