Wasu kungiyoyi na gudanar da tarukan kawo fahimtar juna tsakanin Musulmai da Krista

Wasu kungiyoyi na gudanar da tarukan kawo fahimtar juna tsakanin Musulmai da Krista

- Cibiyar 'Interfaith Dialogue For Peace, IDFP' tayi hadin guiwa da cibiyar 'King Abdul'aziz International Center for Interfaith, KAICIID

- Cibiyoyin biyu sun hadu ne don kai ziyara yankin Mambilla, jihar Taraba, tare da shirya tarukan fadakarwa ga bangarorin guda biyu

- Mrs Liyah A. Solomon, ta bayyyana muhimmancin tashi tsaye don kawo karshen tashin hankula a jihohin Arewa

Yankin Mambilla a jihar Taraba,na daya daga cikin yankunan da ke fuskantar rikice-rikicen kabilanci dana addini, wala Allah wannan ne dalilin da ya sanya wata cibiya ta kasa da kasa, mai fafutukar kawo fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista, ta kai ziyara yankin tare da shirya tarukan fadakarwa ga bangarorin guda biyu.

A jihohin arewacin kasar Nigeria, musamman yankin Arewa-maso-Gabas, an dai yi asarar rayuka da dama da kuma dumbin dukiyar da kudinta basa kiyastuwa, a sanadin tashe tashen hankula da ke da nasaba da rikicin addini da na kabilanci.

Cibiyar 'Interfaith Dialogue For Peace, IDFP' tare da hadin guiwar cibiyar shiga tsakani ta sarki Abdu'aziz, wato 'King Abdul'aziz International Center for Interfaith, KAICIID, sun gudanar da wasu tarurruka da zasu baiwa bangarorin biyu samun fahimtar junansu.

KARANTA WANNAN: Aisha Alhassan: Dalilina na kwashe kujeru, na'urori da saurasu daga ofishin APC na Taraba

Wasu kungiyoyi na gudanar da tarukan kawo fahimtar juna tsakanin Musulmai da Krista
Wasu kungiyoyi na gudanar da tarukan kawo fahimtar juna tsakanin Musulmai da Krista
Asali: Depositphotos

Domin magance matsalolin rikice rikicen addini da kabilanci, cibiyoyin guda biyu sun shirya tarukan kawo fahimtar junan ne a jihohin Filato, Taraba, Benue, Kaduna da kuma jihar Zamfara.

A cikin wadannan tarurrukan ne na kawo fahimtar juna, tawagar cibiyoyin guda biyu, sun gudanar da wani gagarumin taro a yankin Mambilla, cikin garin Gembu, inda suka fara ganawa da basaraken yankin, mai martaba Lamdo Mambilla, Dr. Shehu Audu Baju, daga bisani kuma suka yi taro da masu ruwa da tsaki, tare da jin ra'ayoyin jama'a daga bangarorin guda biyu.

Jami'ar cibiyar wanzar da zaman lafiyan a Taraba, Mrs Liyah A. Solomon, ta bayyyana muhimmancin tashi tsaye don kawo karshen tashin hankula musamman a Jihar Taraba, Borno, Yobe da dai sauran jihohin Arewa-maso-Gabas da lamarin ya fi shafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng