Wani dan acaba da aka kama ya yi luwadi da yara 6 ya hadu da fushin kotu

Wani dan acaba da aka kama ya yi luwadi da yara 6 ya hadu da fushin kotu

Wata kotun Majistare da zamanta a Minna a jihar Niger ta yanke wa wani dan acaba mai shekaru 23, Adamu Mohammed zaman gidan yari na shekaru hudu bayan an same shi da laifin luwadi da yara maza guda shida.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne saboda aikata luwadi wanda ya saba wa sashi na 284 na Penal Code.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Daniel Ikwoche ya shaidawa kotu cewar wani Yusuf Buhari ne ya shigar da kara a caji ofis da ke Chanchaga a ranar 6 ga watan Oktoba.

Wani dan acaba da aka kama ya yi luwadi da yara 6 ya hadu da fushin kotu
Wani dan acaba da aka kama ya yi luwadi da yara 6 ya hadu da fushin kotu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana matsayar ta kan batun karin albashi

Ikwoche ya koka cewar wanda akai karar ya yiwa yaronsa Mohammed mai shekaru 10 dabara inda ya saduwa da shi ta duburarsa a dakinsa da ke kauyen Koropka da ke Minna.

Ya kara da cewar bayan an gudanar da bincike, an gano cewar wanda ake zargin ya aikata luwadin ga wasu yara maza biyar wanda shekarunsa ya kama daga 10 zuwa 12 duk a kauyen na Korokpa.

Mohammed ya amsa laifinsa inda ya kuma roki kotu tayi masa sasauci.

Mai shigar da karar ya roki kotu ta yanke hukunci cikin gagawa kamar yadda sashi na 157 na dokar masu laifi ya bayyana.

A hukuncinsa, shugaban kotun, Nasiru Muazu ya yanke wa Mohammed hukuncin zaman gidan yari na shekaru hudu tare da aiki mai wahala kuma babu zabin biyan tara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel