EFCC: An cigaba da shari’a da tsohon Gwamnan Kano Shekarau

EFCC: An cigaba da shari’a da tsohon Gwamnan Kano Shekarau

Babban Kotun Tarayya da ke Kano ta cigaba da shari’a tsakanin Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da tsohon Gwamnan Jihar na Kano Malam Ibrahim Shekarau.

EFCC: An cigaba da shari’a da tsohon Gwamnan Kano Shekarau
An koma Kotu ta tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau
Asali: Depositphotos

A yau Alhamis ne Kotu ta sake zama da Malam Ibrahim Shekarau da tsohon Ministan harkokin waje Aminu Wali tare da wani Bawan Allah mai suna Mansur Ahmad inda ake zargin su da cin kudi har Naira Miliyan 950.

Ana dai tuhumar tsohon Gwamnan da yin gaba da kudin da su ka kusa kai Naira Biliyan guda a lokacin zaben 2015. Wannan kudi dai sun fito ne daga hannun tsohuwar Ministar man fetur watau Diezani Allison-Madueke.

KU KARANTA: An bincika hawan jinin Ganduje bayan an saki bidiyon zargin karbar cin hanci

Yanzu dai Alkali mai shari’a Lewis Allagoa ya dage karan har sai zuwa karshen watan gobe. Alkali Allagoa ya canji Zainab Bage wanda ta ke duba shari’an a da. Manyan ‘Yan siyasar dai sun fadawa Kotu cewa ba su aikata laifin ba.

Lauyan Hukumar EFCC Johnson Ojogbane yace an ba Ibrahim Shekarau wannan makukun kudi ba tare da ka’ida ba. Shi kuma Lauyan da ke kare su Jibrin Okutekpa ya musanya wannan zargi inda ya kuma nemi aka bada belin su kwanaki.

Kwanaki ne tsohon Gwamna Mal. Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP ya dawo Jam’iyyar APC. Yanzu dai ana tunani zai iya karbe kujerar tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na Sanata a Jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng