Akwai tarin al’ajabi a dorewar Nijeriya bayan shekaru 58 da samun ’yanci - Sagagi
- Wanzuwar Nigeria a matsayin kasa daya duk da irin banbance banbance da ke tsakanin 'yan kasar, ya zama babban jari ga kasar a idon duniya
- Alhaji Sagagi ya yabawa gwamnatin Buhari bisa yadda ta jajurce na yaki da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da wanzuwar zaman lafiya
- A nasa bangaren Alhaji Garba Gaya BIO, shugaban hukumar kula da bin dokokin hanya na Kano ya bayyana cewa ko a fuskar sufuri an samu ci gaba
Kasancewar Nigeria kasa mai dauke da mutane masu banbancin al'adu, addini, kabilu da kuma harsuna sama da 300, akwai abubuwan al'ajabi dangane da kasancewar kasar a matsayin tsintsiya madaurinki daya, masana na ganin cewa zama a matsayin kasa daya da ake ciki a Nigeria babban ci gaba ne da kuma haskawar kasar a idanun kasashen duniya.
Kasashen da ke ikirarin cewa sun samu ci gaba, ciki kuwa har da kasar Singapore da dai sauransu, da ace sune masu dauke da wadannan matsalolin na banbance banbance kabilu, to kuwa da tuni sun wargaje.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Ibrahim Muhammad Sagagi PS babban sakatare a ma'aikatar ayyuka, sufuri da gidaje na jihar Kano, a wani jawabi da ya gabatar yayin taron bukin murnar cikar Nigeria shekaru 58 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka, wanda aka gudanar a Kano.
KARANTA WANNAN: A cikin watanni 7: Gobara ta lakume rayuka 7 da janyo asarar dukiyar N88m a jihar Gombe
Alhaji Muhammad Sagagi ya bayyana cewa la'akari da irin zaman lafiyar da ake yi tsakanin mabanbanta addini da yare a kasar, ya isa zama ishara da kuma amincewa da kwalliya ta biya kudin sabulu, kafin ma a koma ta bangaren ci gaban da aka samu a bangaren Ilimi, tattalin arziki, lafiya da sauran fannonin bunkasa rayuwa a kasar.

Asali: UGC
Alhaji Sagagi ya yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa yadda ta jajurce na yaki da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da wanzuwar zaman lafiya ta hanyar bunkasa sha'anin tsaro, musamman a yankunan da rikicin 'yan tada kayar baya ya shafa.
Shima da ya ke jawabi a yayin taron, Alhaji Aminu Garba Muhammad, babban sakatare a ma'aikatar noma ta jihar Kano, ya ce an cimma gagarumar nasara a bangaren noma, duba da irin himmatuwar gwamnatin tarayya da ta jihar Kani wajen samar da taki da kayan noma ga manoman jihar, da nufin bunkasa harkar noma a Kano da kasar ma baki daya.
KARANTA WANNAN: Farawa da iyawa: Gwamna Fayemi ya mayar da ilimi kyauta a jihar Ekiti
A nasa bangaren Alhaji Garba Gaya BIO, shugaban hukumar kula da bin dokokin hanya na Kano ya bayyana cewa ko a fuskar sufuri an samu ci gaba ma yawa idan a kayi la’akari da yadda a ka samu karuwar tituna a tsakanin Jahohi da kuma cikin Birane wanda a baya samu irin wadannan ba.
Wannan ne ya sa ya jawo hankalin matuka da ke tukin ganganci da kuma wadanda basu kware a tukin ba, da su kasance masu tunawa da rayukan masu amfani da tituna da kuma bin dokokin hanya a koda yaushe, don rage yawan hatsarin da ke afkuwa a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng