Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kano ta fara binciken bidiyon Ganduje
Majalisar dokokin jihar Kano ta bude shafin bincike akan bidiyon dake nuna gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje na karban cin hanci wanda jaridar Daily Nigerian ta wallafa.
Da yake Magana akan cewa lamarin na bukatar duba na gaggawa a ranar Litinin, 15 ga watan Oktoba, wani mamba mai wakiltan mazabar Warawa, Labaran Madari yace majalisar dokokin tayi bincike domin sanin sahihancin bidiyon sannan ta dauki mataki.
Mista Madari yace bidiyon ya zub da kimar gwamnatin jihar, sannan kuma cewa don haka akwai bukatar ýan majalisa su dauki mataki na gaggawa.
Lamarin ya samu goyon baya daga Baffa DanÁgundi, wani mamba dake wakiltan wani bangare na Kano.

Asali: Depositphotos
Da yake martani kan lamarin, kakakin majalisa, Alhassan Rurum ya kafa kwamitin mutun bakwai don suyi bincike kan lamarin sannan su dawo wa majalisar da rahoto.
KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari kainuwa ne dashen Allah – Kungiya
Mambobin kwamitin sun hada da Baffa DanÁgundi (Kano Municipal) a matsayin shugaba, Labaran Madari (Warawa) mamba; Garba Gafasa (Ajingi), mamba; and Zubairu Masu, (Sumaila) mamba.
Sauran sun hada da Ayuba Labaran (Kabo) mamba; Abubakar Galadima (Bebeji), mamba; Garba Yau Gwarmai (Kunchi/Tsanyawa), mamba da kuma; Mujtafa Amin, sakatare.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng