2019: Buhari kainuwa ne dashen Allah – Kungiya
Wata kungiyar magoya bayan Buhari da Osinbajo mai suna Buhari/Osinbajo Mandate Group (BOMG) ta jadadda cewa babu wani jan hankali da jam’iyyar adawa za yi da zai hana Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yin nasarar tazarce a zaben 2019.
Shugaban kungiyar na kasa, Ali Baba Mohammed ya bayyana a wata sanarwa a Abuja cewa hadewa shugaba Buhari kai da aka yi a yanzu duk shirme ne domin shi din kainuwa ne dashen Allah.

Asali: Twitter
Ya jadadda cewa Allah ya zabi Buhari ne domin ya ceto Najeriya daga hannun wadanda suka dakushe ci gabanta da albarkatun ta.
Mohammed wanda ya bayyana cewa kasar ta sha matukar wahala a shekarun baya yace shugabanni barayi basa marhaba da kokarin Buhari wajen ganin ya dawo wa kasar da martabarta daga hannun wadanda suka durkusar da ita.
KU KARANTA KUMA: Ban mara wa Atiku baya ba kan 2019 - Babban malamin addini
Ya kuma yi kira ga ýan Najeriya da su mara washugaban kasar baya domin ganin ya cimma kyakyawar manufarsa akan kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng