Dalilin da yasa nike luwadi da kananan yara - Inji wani katon asara dan shekara 23 a Arewa

Dalilin da yasa nike luwadi da kananan yara - Inji wani katon asara dan shekara 23 a Arewa

Wani matashi dan shekara 23 mai suna Adamu Mohammed da ya gawurta a wajen luwadi da kananan yara a karamar hukumar Chanchaga, jihar Neja dake a Arewa ta tsakiyar Najeriya ya bayyana dalilin da yasa ya zabi yin luwadi a rayuwar sa.

Adamu wanda yanzu haka yake a hannun 'yan sandan jihar, ya shaidawa 'yan jarida cewa ya zabi zama dan luwadi ne sakamakon kasantuwar maza basu yin ciki kamar mata.

Dalilin da yasa nike luwadi da kananan yara - Inji wani katon asara dan shekara 23 a Arewa
Dalilin da yasa nike luwadi da kananan yara - Inji wani katon asara dan shekara 23 a Arewa
Asali: UGC

Legit.ng ta samu cewa 'yan sandan dai sun cafke shi ne a lokacin da yake kokarin tserewa ya bar garin bayan da wani uban yaron da yayi luwadin da shi ya kai rahoton sa wajen 'yan sandan karamar hukumar ta Chanchanga ranar Juma'ar da ta gabata.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kano sun aike da takardar sammaci suna gayyatar dan takarar kujerar gwamnan Kano, Alhaji Sagir Abdullahi Takai bisa mutuwar wani tsoho mai shekaru 70 a duniya lokacin da ya ke gudanar da gangami.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan SP Magaji Majiya ya bayyana cewa suna sa ran dan takarar zai mika kansa ga kwamishin 'yan sandan jihar don girmama gayyatar da suka yi masa da kuma ansa wasu 'yan tambayoyi a ranar Litinin mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel