Akwai kyakkyawar makoma ga Nigeria, ku zabi 'yan takarar da suka cancanta - Matar Atiku

Akwai kyakkyawar makoma ga Nigeria, ku zabi 'yan takarar da suka cancanta - Matar Atiku

- Titi, matar dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ta bukaci mata su zabi shuwagabannin da suka cancanta a zaben 2019

- Matar dan takarar shugaban kasar karkashin PDP, ta ce tana da yakinin cewa har yanzu akwai kyakkyawar makoma ga Nigeria

- Ta kuma bukaci mata da su dage wajen tarbiyar yaransu don basu damar rike manyan mukaman gwamnati idan sun girma

Titi Abubakar, matar dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a ranar Asabar, 13 ga watan Oktoba, ta bukaci mata da su zabi shuwagabannin da suke ganin sun cancanta a babban zabe na 2019.

Abubakar, wacce kuma ita ce ta assasa gidauniyar da ke fafutukar kawo karshen safarar mata da kananan yara tare da tursasasu yin bauta (WOTCLEF), a wani taron matan zumunta na majami'ar Anglican a Abuja, ta ce ta hakan ne za a samar da shuwagabanni masu jin tsoron Allah da ke son ci gaban kasar.

KARANTA WANNAN: Idan har na zama shugaban kasa: Ba zan dauki watanni 6 kafin bayyana mukarrabaina ba- Atiku

Ta kuma kalubalanci matan da su daure wajen ganin sun tarbiyantar da yaransu akan hanyar da ta dace, tana mai cewa. "Ta hakan ne zamu samar da yara masu kishin kasa idan sun girma, wadanda za su kawo ci gaba mai ma'ana, tabbas akwai kyakkyawar makoma akan hakan."

Akwai kyakkyawar makoma ga Nigeria, ku zabi 'yan takarar da suka cancanta - Matar Atiku
Akwai kyakkyawar makoma ga Nigeria, ku zabi 'yan takarar da suka cancanta - Matar Atiku
Asali: Depositphotos

A nata jawabin, Nkasiobi Okoh, matar shugabar majami'ar, wacce kuma har ila yau ta ke shugabar kungiyar iyaye mata ta majami'ar, ta bukaci mata da su kasance a cikin shirin bada dukkanin lokaci da iliminsu ga koyarwar Isah mai ceto.

Ta kuma bukaci matasa da su kauracewa yan siyasa masu amfani da su don bangar siyasa musamman ganin yadda babban zaben 2019 ke ci gaba da gabatowa. Ta sanar da su cewa hakkinsu ne su fita ranar zabe su kad'a kuri'a ga wanda suke so ya shugabance su.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel