Atiku fa guguwa mai karfin gaske - Jigo a APC

Atiku fa guguwa mai karfin gaske - Jigo a APC

- Wani jigo a jam'iyyar APC daga jihar Neja, Mohammed Santuraki ya gargadi jam'iyyarsa ta zage damtse game da zaben 2019

- Santuraki ya ce ya zama dole jam'iyyar APC ta tashi tsaye domin PDP ta tsayar da gagarumin dan takarar da za'a fafata dashi a 2019

- Ya shawarci jam'iyyar da kada tayi kasa a gwiwa wajen yakin neman zabe kafin shekarar 2019

Atiku fa guguwa mai karfin gaske - Jigo a APC

Atiku fa guguwa mai karfin gaske - Jigo a APC
Source: Depositphotos

Wani jigo a jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Niger, Mohammed Santuraki ya gargadi jam'iyyar ta zage damtse muddin tana son tayi nasara a babban zaben shugabancin kasa na 2019.

A hirar da Santuraki ya yi da kamfanin dillancin labarai NAN a ranar Asabar a Suleja, jigon ya ce dole APC ta sake gyara tare da hada kan 'yan jam'iyyar idan tana son tayi nasara.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 6 da ake amfani da goro da ya dace ku sani

Ya ce akwai rikice-rikice da dama da suka taso a yayin gudanar da babban taron gangamin jam'iyyar da zaben fidda gwani na jihohi kuma ya kamata a warware wannan matsalolin cikin gagawa.

Ya kara da cewar, nasarar da Atiku ya yi na lashe tikitin takarar jam'iyyar PDP abu ne da ya kamata ya janyo hankalin 'ya'yan APC su hada kansa waje guda.

"Ko mun amince ko ba mu amince ba, Atiku Abubakar dan takara ne mai karfi duk da cewa bashi da nagarta.

"Cikin mako daya da zabensa a matsayin dan takara, ya zabi shugabanin kungiyar yakin neman zabensa kuma ya zabi mataimakinsa. A ra'ayina wannan alama ce da ke nuna APC ya kamata da zage damtse domin lokaci na kurewa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel