Najeriya ba ta siyarwa ba ce – APC ga Atiku

Najeriya ba ta siyarwa ba ce – APC ga Atiku

Jam’iyyar All Progressives Congress(APC) mai mulki ta ja kunnen ‘yan Najeriya da su yi wa kansu karatun ta natsu akan dan takarar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tsayar da zai fafata da shugaba Muhammadu Buhari wato, Atiku Abubakar.

Babban sakataren labaran APC, Yekini Nabena ne ya bayyana haka a shimfidaddiyar takarda da ya saka wa hannu da ya kunshi sakon taya murna ga Atiku da yi masa tuni cewa Kasa Najeriya fa ba ta siyarwa bace.

Najeriya ba ta siyarwa ba ce – APC ga Atiku
Najeriya ba ta siyarwa ba ce – APC ga Atiku
Asali: Depositphotos

“Babu shakka ana ikirarin cewa Atiku gawurtaccen attajiri ne wanda ke ganin wannan dukiya da ya mallaka ko da karfin tsiya za ta siya masa kujerar mulkin Najeriya musammam ganin yadda ake ta yadawa ya yi ruwan daloli a wajen zaben fidda dan takara da aka yi.

“Mu hakan bai dame mu ba ko kadan saboda yunwar sa na dole sai ya mulki Najeriya ba tun yanzu bane ya fito fili.

“Atiku ya canja jam’iyya har sau uku yana neman haka. Kuma mun sane yunwa sa ba zai haifar wa Najeriya da da mai ido ba."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Obasanjo na ganawar sirri da Afenifere

Sannan kuma Nabena ya yi kira ga mutanen Najeriya da su yi karatun ta natsu su karkato da hankulan su su duba irin shugaban kasar da za su zaba.

Wanda shi gaba daya dukiya da arziki ce takamar sa ko kuma shugaban da talakawa ne a zuciyar sa, wanda burin sa ya shimfida kasar nan a tafarkin gaskiya da zai dore.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel