Yanzu Yanzu: Yan sanda sun rufe sakatariyat APC bayan fusatattun matasa sun yi zanga-zanga a Abuja

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun rufe sakatariyat APC bayan fusatattun matasa sun yi zanga-zanga a Abuja

- Jami’an tsaro sun rufe sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki

-Hakan ya biyo bayan zanga-zanga da fusatattun matasa suka gudanar a sakatariyar APC dake Abuja

- Sun yi zanga zanga-zangan ne akan tsarin zabar wanda zai wakilci yankin a majalisar dattawa

Jami’an tsaro sun rufe sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki biyo bayan wani zanga-zanga da matasa suka yi akan yin amfani da zaben fidda gwani na wakilai wajen tsayar da dan takarar sanat na babba bhirnin tarayya.

Fusatattun matasa da ake ganin magoya bayan daya daga cikin yan takarar dake neman tikitin takarar kujeran sanata a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a birnin tarayya Abuja sun mamaye babban sakatariyar APC na kasa inda suke gudanar da zanga-zanga.

A cewar masu zanga-zangar yin amfani da zaben fidda gwani na wakilai daidai yake ga cewar dan asalin yankin ba zai samu tikitin ba.

Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa mamaye sakatariya APC a Abuja
Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa mamaye sakatariya APC a Abuja
Asali: Depositphotos

Matasan dake dauke da muggan makamai daban-daban sun rufe mashigi da hanyar fita na unguwar Blantyre inda anan ne sakatariyar yake.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a bayan cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ahmad Lawan a ranar Laraba, 3 gawatan Oktoba ya mallaki tikitin jam’iyyar Progressives Congress (APC) domin takarar kujerar sanata a yankin Yobe ta arewa a zabe mai zuwa.

Alhaji Umar Kareto, jami’an zaben yace wakilai 1,865 aka tantance a mazabar shugaban majalisar inda ya samu kuri’u 1,702 yayinda aka soke 12.

KU KARANTA KUMA: Hukumar yaki da rashawa ta tasa keyar Dakingari har gaban kan satar N1, 094, 320,000

Lawan wanda ya fito bai da abokin hamayya yayi godiya ga mutanen da suka amince da shi domin ya wakilci yankin a majalisar dattawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel