Manyan matsafa 13 a Arewa sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya

Manyan matsafa 13 a Arewa sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya

Jami'an 'yan sandan Najeriya, shiyyar jihar Kwara sun sanar da samun nasarar cafke wasu gawuratattun matsafa 'yan kungiyar asirin nan ta Badoo da suka addabi al'ummar jihar.

Manyan matsafa 13 a Arewa sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya
Manyan matsafa 13 a Arewa sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yan bindiga sun sace motoci 5 cike da mutane a Birnin Gwari

Majiyar mu ta Tribune, ta tabbatar mana da cewa jami'an 'yan sandan sun cafke matsafan ne bayan wani samame da suka kai masu sakamakon bayanan sirri da suka samu daga wasu masu kishin kasa.

Legit.ng ta samu cewa jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar Ajayi Okasanmi ya bayyana cewa suna nan suna bincike a kan su kuma da sun kammala za su kai su kotu domin a yanke masu hukunci.

Mai karatu dai idan bai manta ba 'yan kungiyar asirin a watannin baya sun addabi al'ummar jihar da ma makwafta inda sukan kashe jama'a su kuma yi tsafi da wasu sassa na jikin su.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake kula da shiyyar jihar Ribas sun sanar da samun nasarar cafke wani babban malamin addinin kirista da kuma wasu mata masu ciki da suka kai akalla 16 bisa zargin cinikayyar jarirai.

Wannan dai kamar yadda muka samu daga bakin kwamishinan 'yan sandan jihar Zaki Ahmed, ya biyo bayan wani samame ne da jami'an 'yan sandan suka kai a wani gidan dake zargin ana yiwa mata ciki sannan kuma su saida jariran a garin Fatakwal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewarku tare da mu

Asali: Legit.ng

Online view pixel