An Yi wa Ado Aleiro Babbar Barna da Kazamin Fada Ya Barke tsakanin 'Yan Bindiga a Zamfara
- Rahotanni sun ce sama da ’yan bindiga 40 sun mutu a rikicin cikin gida tsakanin ɓangarorin ’yan bindiga a gabashin yankin Mada na Jihar Zamfara
- Ana zargin Sanata, wanda aka ce ƙanin fitaccen jagoran ’yan bindiga Ado Allero ne, yana cikin waɗanda suka mutu
- Rikicin na da alaƙa da takaddama kan iko da yankuna, shugabanci da fafatawa kan albarkatu tsakanin ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Rahotanni sun bayyana cewa rikicin cikin gida tsakanin wasu ɓangarorin ’yan bindiga a gabashin yankin Mada na Jihar Zamfara ya yi sanadin mutuwar mayaƙa sama da 40.
Daga cikin wadanda aka kashe har da wani da ake zargin ƙanin fitaccen jagoran ’yan bindiga, Ado Allero, ne. An bayyana mutumin da ake zargin ya mutu da laƙabin “Sanata”.

Source: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoban 2026.
Majiyoyin tsaro da bayanan mazauna yankin sun ce arangamar ta faru ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin saɓani tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindigar da ke gudanar da ayyukansu a yankin.
Sai dai har yanzu ba a bayyana ainihin abin da ya haddasa rikicin ba a tsakanin kungiyoyin 'yan bindigan masu gaba da juna.
Ana zargin an kashe ƙanin Ado Aleiro
Daga cikin waɗanda rahotanni suka ce sun mutu akwai Sanata, wanda aka bayyana a matsayin ƙanin Ado Allero, ɗaya daga cikin fitattun shugabannin ’yan bindiga da ke aiki a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da mutuwar Sanata ta wata sanarwa a hukumance ba.
Idan aka tabbatar da rasuwarsa, hakan na iya yin tasiri ga ƙungiyar da ke da alaƙa da Ado Aleiro, musamman idan lamarin ya ƙara tsananta saɓanin da ake zargin ya riga ya shiga tsakanin ɓangarorin ’yan bindigar.
Bayanan farko sun nuna cewa rikicin ya faru ne tsakanin wasu masu ɗauke da makamai daga cikin ƙungiyoyin ’yan bindigar da kansu.
Abin da ke rura cikin tsakanin 'yan bindiga
Rikice-rikicen cikin gida tsakanin ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka a yankin Arewa maso Yamma na iya kasancewa sakamakon takaddama kan ikon mallakar yankuna.
Haka kuma, rashin jituwa kan shugabanci da fafatawa wajen samun albarkatu na daga cikin abubuwan da ake dangantawa da ƙaruwar saɓani tsakanin ƙungiyoyin.
Sai dai ba a bayyana ko ɗaya daga cikin waɗannan dalilai ne ya haddasa arangamar ta baya-bayan nan a yankin Mada ba.
Ana sa ran samun ƙarin bayani yayin da majiyoyi masu sahihanci ke ci gaba da tattara bayanai kan lamarin.
'Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum biyar, ciki har da jariri mai kimanin wata guda a jihar Kaduna.
"Yan bindigan dauke da makamai sun sace mutanen ne a Mararaban Kajuru, da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng

