Zaben fitar da gwani: Atiku da Saraki sun bayyana ra'ayin su game da zabar Fatakwal

Zaben fitar da gwani: Atiku da Saraki sun bayyana ra'ayin su game da zabar Fatakwal

- Atiku da Saraki sun bayyana ra'ayin su game da zabar Fatakwal matsayin wurin fitar da gwani

- Atiku yace ya amince, Ribas gida ne a gare shi

- Saraki ma ya ce bai da matsala da hakan

Daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa labaran da ake yadawa na cewa bai ji dadin kai zaben fitar da gwanin su ba a garin Fatakwal ba gaskiya bane.

Zaben fitar da gwani: Atiku da Saraki sun bayyana ra'ayin su game da zabar Fatakwal
Zaben fitar da gwani: Atiku da Saraki sun bayyana ra'ayin su game da zabar Fatakwal
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi manyan kasar nan tatas

Atiku wanda yace shi garin Fatakwal kusan gida ne a gare shi ya bayyana cewa baya ma bukatar masauki ko wani tsaro na musamman domin kuwa a yi wani bangare na rayuwar sa a garin a shekarun baya.

Legit.ng ta samu cewa haka ma shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki shima ya ce yayi na'am da yin zaben a garin na Fatakwal inda yace tabbas sune dukan su suka amince da hakan bayan wata tattaunawa mai tsaro da suka gudanar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a baya gwamnan jihar ta Ribas dake zaman daya daga cikin ginshikan jam'iyyar ta PDP yayi barazanar dagargaza jam'iyyar idan har aka dauke wurin yin gangamin daga jihar Ribas.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamna na jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar APC kuma tsohon shugaban hukumar nan da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Nuhu Ribadu ya karyata batun janyewar sa daga takarar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban kamfe din sa, Salihu Bawuro ya fitar dauke da sa hannun sa a garin Yola, babban birnin jihar ta Adamawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel