Wutar rikicin jam'iyyar PDP na kara ruruwa a jihar Katsina sakamakon tsayar da Yakubu Lado

Wutar rikicin jam'iyyar PDP na kara ruruwa a jihar Katsina sakamakon tsayar da Yakubu Lado

- Rikici na ci gaba da ruruwa a jam'iyyar PDP sakamakon tsayar da Sanata Yakubu Lado a matsayin dan takarar kujerar gwamna a Katsina

- Masu adawa da zaben Lado sun ce sun dawo daga rakiyar shuwagabannin jam'iyyar a matakin jihar

- Akalla 'yan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar guda 5 ne suka nuna tsantsar kiyayyarsu ga wannan hukunci

Wutar rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP reshen jihar Katsina na ci gaba da ruruwa, a yayin da 'yan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar ke ci gaba da adawa da hukuncin shuwagabannin jam'iyyar na tsayar da Sanata Yakubu Lado a matsayin dan takarar gwamnanta ta hanyar nad'i ba tare da zaben fitar da gwani ba.

Wasu 'yan takara biyu, Abdullahi Garba Faskari da kuma Sada Ilu a cikin wata sanarwa daga Alhaji Dauda Kurfi, daraktan kungiyar kamfe ta Abdullahi Garba Faskari AGF, a madadin 'yan takarar, ya ce sakamakon amincewa da zaben nadin dan takara, mun amince da sharudda na cewa wani dan takara ba zai biya kudi don a zabe shi ba.

Sai dai ya ce sun gano cewar dukkanin sharuddan da suka gindayawa shuwagabannin jam'iyyar sun hau ta kansu sun zaune ba tare da amfani da ko daya ba, kuma da masaniyar shugaban jam'iyyar na jihar da wasu jami'anta.

Wutar rikicin jam'iyyar PDP na kara ruruwa a jihar Katsina sakamakon tsayar da Yakubu Lado
Wutar rikicin jam'iyyar PDP na kara ruruwa a jihar Katsina sakamakon tsayar da Yakubu Lado
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga rundunar sojin sama bisa rasuwar Baba Ari

Sanarwar ta ce: "A don haka ne, muka yi watsi da wannan sakamako; haka zalika mun dawo daga rakiyar shuwagabannin jam'iyyar a matakin jihar, kuma ba zamu jure sa hannu a zaben fitar da gwani ba har sai idan uwar jam'iyyar ta kasa ta sanya hannu don ayiwa kowa adalci."

"Muna amfani da wannan kafar wajen bukatar shelkwatar jam'iyyar ta kasa da ta yi gaggawar sanya baki akan matsayar jam'iyyar a jihar Katsina, ma damar ana so a yiwa mambobin jam'iyyar dama daukacin al'umar jihar Katsina adalci," a cewar sanarwar.

Legit.ng ta samu rahoton cewa tuni dai dama wasu 'yan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar, Abdullahi Umar Tsauri, Musa Nashuni da kuma Arc. Ahmed Aminu Yar'adua suka yi 'tir!' da wannan zabe na tsayar da Lado a matsayin dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel