Dandalin Kannywood: Ni yanzu na girmi aure, sai dai in aurar da 'ya'ya na - Hadizan Saima

Dandalin Kannywood: Ni yanzu na girmi aure, sai dai in aurar da 'ya'ya na - Hadizan Saima

- Jaruma Hadizan Saima ta bada labari kan auren ta na farko

- Tace shekarun ta 20 a gidan miji

- Tace ita yanzu ita sai dai ta aurar da 'ya'yan ta

Jarumar nan ta masana’antar Kannywood wadda ta shahara wajen fitowa a matsayin uwa a fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood da dama watau Hadizan Saima ta bayyana dalilin ta da ya sa ya zuwa yanzu bata marmarin sake yin aure kwata-kwata.

Dandalin Kannywood: Ni yanzu na girmi aure, sai dai in aurar da 'ya'ya na - Hadizan Saima
Dandalin Kannywood: Ni yanzu na girmi aure, sai dai in aurar da 'ya'ya na - Hadizan Saima
Asali: Facebook

KU KARANTA: Mawaki Ado Gwanja zai angwance

Fitacciyyar jarumar wadda ta ce ta shafe akalla sama da shekaru ashirin a gidan miji ta ce ita yanzu kam sai dai ta aurar da nata 'ya'yan amma ita ta ci girma don kuwa an sha ta ta warke inda game da maganar ta aure ce.

Legit.ng ta samu cewa Hajiya Hadiza, wadda yanzu haka take cikin jerin taurarin ta ke matukar haskawa a farfajiyar masana’antar ta bayyana cewa ita yanzu ta girma kuma indai ana maganar aure to ita sai dai ta bayar da lekca akan sa saboda irin dadewar da tayi a gidan miji.

Haka zalika jarumar ta bayyana cewa tana mamakin yadda mutane ke yiwa masu sana'a irin tasu tsogumi game da maganar aure.

Ta kara da cewa ita ta yadda da cewa aure shine suturar dukkan 'ya mace amma kuma ta ce komai lokaci ne da shi kuma dukkan mace tana son tayi aure.

A wani labarin kuma, Fitaccen jarumin nan da kan fito a fina-finan Hausa na masana'antar Kanyywood kuma mawaki da tauraruwar sa ke haskawa a wannan zamanin, Adamu Isa wanda aka fi sani da Gwanja ya shirya tsaf domin zama ango a ranar 13 ga watan da ya gabata na Oktoba.

Kamar yadda muka samu, mawakin Ado Gwanja dai zai auri masoyiyar sa ce mai suna Maimuna Kabir Hassan kuma ana sa ran daura auren ne a garin Kano a ranar ta 13 ga watan gobe da misalin karfe 11 na safe a kan titin zuwa gidan Zoo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel