An Bayyana Wurin da Wata Mata ta dauko cutar Ebola Ta Shigo da Ita Najeriya

An Bayyana Wurin da Wata Mata ta dauko cutar Ebola Ta Shigo da Ita Najeriya

  • Gwamnatin Switzerland ta tabbatar da cewa matar da aka tabbatar tana dauke da cutar Ebola a Najeriya, matar wani jami'inta ne
  • An ce matar ta fara nuna alamun cutar ne bayan tafiya Uganda, inda ake zargin ta kamu da cutar kimanin makonni biyu da suka wuce
  • Hukumomin lafiya na Najeriya da na Afirka na gudanar da bincike kan yadda cutar ta bazu, yayin da Kenya ta tabbatar da ƙarin mutane takwas da suka kamu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gwamnatin Switzerland ta bayyana cewa matar wani jami’in diflomasiyyarta da ke zaune a Abuja, wadda aka haifa a Uganda, ita ce mai cutar Ebola da aka tabbatar a Najeriya.

Idan baku manta ba, an tabbatar da wata mata da ta dawo daga kasar Uganda na dauke da cutar Ebola a Abuja, inda hukumomi suka killace ta tare da wadanda suka yi huldada ita.

Kara karanta wannan

Abin bakin ciki: Matashi ya kashe abokinsa da suke aiki wuri 1 kan gardamar siyasa

Ebola.
Yadda ke gwajin cutar Ebola a dakin gwaje-gwaje Hoto: Getty images
Source: Getty Images

A wace ƙasa matar ta dauko Ebola?

A cikin wata sanarwa da ta aikawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Alhamis, Ma’aikatar Harkokin Wajen Switzerland ta ce ana zargin matar ta kamu da cutar ne a lokacin wata tafiya da ta kai Uganda.

Ma’aikatar ta bayyana cewa matar ta shafe kusan mako guda tana karɓar magani a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja bayan ta fara nuna alamun cutar.

Sanarwar ta ce:

"Ana zargin ta kamu da cutar ne a lokacin da ta je Uganda kimanin makonni biyu da suka wuce.”

Gwamnatin Switzerland ta ƙara da cewa mijin matar, wanda ya yi tafiya tare da ita, yana killace a halin yanzu, amma bai nuna alamun cutar ba.

Najeriya ta tabbatar da cutar Ebola

A ranar Talata ne Najeriya ta tabbatar da bullar cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo a karon farko, bayan gwaje-gwajen dakin bincike sun gano ƙwayar cutar a jikin wata mata da ta shigo ƙasar kwanan nan.

Kara karanta wannan

Ebola: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan 'yiwuwar' hana taruwar jama'a

Jean Kaseya, babban daraktan Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), ya ce an haifi matar ne a Uganda, kuma ta je ƙasar kafin ta dawo Abuja tare da mijinta a ranar 3 ga Oktoba.

Kaseya ya ce hukumomin lafiya suna binciken ko matar ta kuma je Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), ko ta yi mu’amala da wani daga ƙasar, ko kuma ta ziyarci wasu wurare a wajen Kampala, babban birnin Uganda.

Ebola.
Likitoci da ke kula da wadanda suka kamu da cutar Ebola Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Tun da farko, hukumomin lafiya na Uganda sun yi ikirarin cewa matar ’yar Najeriya ce, kuma ta je gabashin DRC kasuwanci kafin ta bi ta Uganda a farkon watan Oktoba.

Charles Olaro, babban daraktan kula da ayyukan lafiya na Uganda, ya ce matar ba ta nuna alamun cutar ba a lokacin da take ƙasar, sai dai ta fara rashin lafiya bayan ta isa Najeriya.

Olaro ya bayyana cewa kasancewar matar ta bi ta Uganda ba ya tabbatar da cewa a can ta kamu da cutar, yana mai cewa ana ci gaba da binciken wurin da ta kamu da ita.

Babu rigakafin Ebola a Afirka

Kun ji cewa shugaban hukumar CDC ta nahiyar Afirka ya yi magana kan rashin samar da magani/rigakafin nau'in cutar Ebola da ta shiga Najeriya.

Ya ce nuna halin ko in kula na kasashen duniya ne ya sa har yau babu rigakafin da aka amince da shi kan nau’in cutar Ebola ta Bundibugyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262