Dandalin Kannywood: Soyayyar Maryam Yahaya da wani furodusa ta fito fili
- Soyayyar Maryam Yahaya da wani furodusa ta fito fili
- Ana kishin kishin din tana soyayya ne da furodusa Abubakar Bashir Maishadda
- Maryam Yahaya a baya ta saka hotunan su a tare
Wata shakuwa da ake zargin tuni ta rikide ta koma soyayya mai karfi ta shiga tsakanin daya daga cikin matasan jarumai mata a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood dake tasowa, watau Maryam Yahaya da wani mashiryin shirin fina-finai, Abubakar Bashir Maishadda.

Asali: Instagram
KU KARANTA: Wani maciji ya cafke barawon katifa
Masu bibiyar harkokin dake gudana a masana'antar fina-finan ta Hausa dai musamman ma a bayan fage sun tabbatar mana da cewa a 'yan watannin nan wata alaka mai karfi da ake tunanin soyayyace ta shiga tsakanin mutanen biyu.
Legit.ng a wani dan binciken da ta gudanar ita ma ta gano cewa kusan dukkan fina-finan da mashiryin fim din ke fitar wa akwai jarumar a ciki kuma ma takan taka muhimmiyar rawa a ciki.
Haka zalika ma dai soyayyar tasu ta kara fito fili karara ne a ranar 14 ga watan Satumba inda aka tsinkayi jarumar Maryam ta dora wasu hotuna a shafinta na dandalin zumuntar zamani na Instagram ita da Furodusa Maishadda sanye da zobuna iri daya wanda daga baya ta gogesu.
Maryar Yahaya dai na daya daga cikin jarumai mata dake tashe yanzu a masana'antar Kannywood tun bayan wata muhimmiyar rawa da ta taka a cikin shirin fim din Mansoor.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng